Da Akwai Miliyoyin Yan Najeriya Da Ke Bukatar Yin Rajistan Katin Zabe – Dan Majalisa Fulata

0
343

Daga Bashir Bello, Kaduna.

DAN Majalisar Tarayya dake wakiltar Mazabar Birniwa/Guri/da shiyyar Kiri-Kasamma a Jihar Jigawa, Honarabul Abubakar Fulata ya bayyana cewa da akwai bukatar Hukumar Zabe ta kasa (INEC) da ta kara wa’adin yin rajistan katin zabe domin miliyoyin yan Najeriya su samu damar shiga cikin tsarin yin zaben.

Honarabul Abubakar Fulata wanda ya ke Shugaban kwamitin Dokoki da harkokin kasuwanci ayayin da yake yiwa manema labarai karin bayani game da matsayar Majalisar Tarayya a kan yin aikin katin Zaben, ya bayyana cewa biyo bayan wani kudirin da kwamitin da ke kula da harkokin ta gabatar, Majalisar ta aminta da kudirin.

Ya kara da cewa bayan sauraren kudirin da kwamitin ta gabatar a satin daya gabata a zauren Majalisar, an umarci kwamitin da ta aika wa hukumar Zaben ta kasa (INEC) da bukatar ita Majalisar na neman karin lokacin yin aikin rajistan domin sauran Miliyoyin Yan Najeriya su samu damar yin rajistan.

Ya ce “abin da muka gudanar a Majalisar a wannan karon shi ne sauraren bayanan kwamitin domin sanin halin da ake ciki na neman karin lokaci na watanni biyu saboda wasu Miliyoyin al’umma su samu damar yin rajistan da sauran yan gyare-gyaren da ba za a rasa ba, domin a satin daya gabata shugabar kwamitin ta kawo kudirin, kuma Majalisar ta aminta da yin hakan.”

Acewarsa, a yanzu Majalisar na sauraren jin amsar hukumar zaben ta kasa (INEC) ta bakin kwamitin da aka nada domin tuntubar hukumar wanda kuma ita Majalisar ta ke saran cewa hukumar Zaben zata aminta da bukatunsu na karin lokacin har zuwa watanni biyu nan gaba kamin a rufe aikin yin rajistan.

A karshe, Dan Majalisar Tarayyar Honarabul Abubakar Fulata, ya Jaddada bukatar Majalisar na rokon hukumar zaben ta kasa (INEC), da ta yi kokarin karin wa’adin yin rajistan domin sauran al’umma su amfana duk da cewa ita hukumar ta yi hakan har sau biyu.

Leave a Reply