APC Ta Tsayar Da Munira Suleiman A Matsayin Yar Takarar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna A Mazabar Lere

0
585

Daga; Isah Ahmed, Jos.

WAKILAN jam’iyyar APC masu zabe, na Mazabar Lere ta gabas, dake Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, sun zabi fitatciyar mai taimakawa marayu da mata da matasan nan kuma Zinariyar Saminaka, Munira Suleiman Tanimu, a matsayin yar takarar kujerar wannan mazaba, a zabe mai zuwa na shekara ta 2023. Wakilan jam’iyyar ta APC sun zabi Zinariyar ta Saminaka ne a daren jiya a garin Saminaka.

Da yake bayyana sakamakon zaben, babban jami’in da ya gudanar da zaben Muhammed Zaiyanu, ya bayyana cewa a wannan zabe da aka gudanar, Munira Sulaiman Tanimu ta sami kuru’u 27,
Yusuf Umar Maskawa ya sami kuru’u 2, a yayin da Musa Garba Aluwalo ya sami kuri’a 1. Don haka ya ce Munira Suleiman Tanimu ce ta lashe wannan zabe.

Da take jawabi, bayan bayyana sakamakon zaben , Munira Sulaiman Tanimu ta bayyana cewa wannan wata babbar rana ce ta farin ciki a gareta, musamman ganin wannan takara da ta fito ita ce ta uku.

Ta ce a yau Allah ya kaddara ta sami masara zama yar takarar jam’iyyar APC na wannan mazaba. Don haka ta mika godiyarta ga dukkan yan wannan jam’iyya kan goyan bayan da suka bata, aka yi wannan zabe cikin kwanciyar hankali.

Ta yi kira ga wadanda suka yi takara da su zo su hada kai, domin a sami nasarar lashe wannan zabe.

Shi ma da yake jawabi, daya daga cikin wadanda suka yi wannan takara Yusuf Umar Maskawa, ya yi kira ga sauran wadanda suka yi wannan takara, da su hada kai, da wannan yar takarar da ta sami nasara, domin ganin jam’iyyar APC ta ci wannan zabe, a zabe mai zuwa na shekara ta 2023.

Leave a Reply