Surayya Aminu Za Ta Bunkasa Harkokin Matasa Da Wasanni

0
367

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

BABU shakka, Hajiya Surayya Aminu wadda aka fi sani da ” Sai Mama ” zata iya kawo ci gaba mai kyau a famnin ci gaban matasa da kuma wasanni idan aka bata dama daga Gwamnatin Jihar kano.

Wannan bayani ya biyo bayan wani bincike da aka gudanar na yadda Hajiya Surayya Aminu ta ke matukar bada gudummawar ta ga gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje tun lokaci mai tsawo.

Kasancewar ta mace kuma mai kaunar ci gaban jihar kano, Hajiya Surayya Aminu Sai Mama, tana kuma da kwarewa a harkar bunkasa Harkokin Matasa da wasanni duba da yadda a yanzu haka take cikin kunshin shugabannin gudanarwa a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Mafi yawan mutanen da aka tattauna dasu, sun bayyana Hajiya Surayya Aminu sai Mama a matsayin mace mai kaunar ci gaban jihar kano da gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje duba da yadda ta ke kokari wajen rike amanar da aka bata a duk in da ta sami kanta.

Don haka nema matasa da masu yin sharhi kan al’amuran matasa da wasanni suka baiwa gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje shawarar da ya baiwa Hajiya Surayya Aminu mukamin kwamishinar matasa da wasanni ta yadda za ta kara kawo ci gaba mai albarka da bunkasa Zaman lafiya da kaunar juna a jihar kano dama kasa baki daya.

Leave a Reply