Tsaro: Kungiyar Masu Dauko Rahotanni Ta NUJ Kaduna Ta Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani

0
295

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR masu Dauko Rahotanni karkashin Jagorancin Kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, ta gudanar da wani taron karawa juna sani kan harkar tsaro da bayar da lambar yabo ga wasu fitattun al’umma bisa gagarumin gudunmuwar da suka bayar ta fannin kokarin wanzar da zaman lafiya Jihar.

Taron wanda ya gudana a gidan Arewa na Sardauna dake Kaduna a ranar talata, mai taken “Tackling Security Challenges: The Role Of Media,” an shirya shi ne don tunatar da yan Jaridu mahimmancinsu da aikin Jarida a cikin al’umma, kana da kokarin sanya fikira da hikima a cikin aikin nasu na daukar rahotanni yayin gudanar da harkokin aikin Jaridar.

Babban bako mai jawabi a wajen taron, kuma Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Mista Samuel Aruwan, ya bayyana mahimmanci aikin Jarida da yan Jaridun a matsayin wani babban Kalubale wanda zai iya zama wata sila na warware mafi akasarin matsalolin da ake fuskanta na tsaro a kasar baki daya.

Mista Aruwan, ya kara da cewa wajebi ne yan Jaridu su kasance masu kokarin yin gaskiya da bin gaskiya ta fannin gudanar da ayyukansu, ba tare da bin manufofin raba kan jama’a da kan iya zama barazana ga ci gaban al’umma ba.

Ya ce “A matsayinmu na ’yan wannan babbar kungiyar kafafen yada labarai, tilas ne mu watsar da labaran raba kan jama’a da masu neman mulki suke tallatawa na tsawon shekaru da dama. Ba za mu iya ƙara yin sakacin amsar duk sakonnin ɓatanci da ɓata ɗan adam ba. Kada mu amince ra’ayin yan siyasa mai dauke da kabilanci.”

Kwamishinan ya kara jaddada bukatar masu aikin su shiga aikin jarida da ya shafi gaskiya da daidaito da kuma bayanan gaskiya.

Har ila yau yana son ’yan jarida su nisanci wakilcin yanke hukunci kuma su bayyana gaskiya ba tare da wuce gona da iri ba.

Aruwan, ya jaddada cewa, kafafen yada labarai na iya taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, ta hanyar aikin jarida mai inganci.

Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa gwamnati a nata bangaren, za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro, tare da hada kai da ‘yan kasa yadda ya kamata domin magance matsalolin tsaro a fadin Jihar.

Mista Aruwan, ya yabawa wadanda suka shirya taron bisa yadda suka nuna kwazo wajen ganin sun taimaka an tafiyar da harkokin tsaro da hana tada kayar baya a Jihar, tare da ba da lambar yabo ga wasu al’ummar da suke kokarin tabbatar da zaman lafiya, kana ya sake jaddada bukatar ‘yan jarida su ci gaba da gudanar da ayyukansu na zaman lafiya don samar da tsaro.

Tun da farko a jawabin maraba, shugaban riko na kungiyar masu dauko rahotannin, Mista Moses Kolo ya bukaci takwarorinsa da su gujewa dauko rahotannin da ba a tabbatar da su ba musamman kan hare-hare da sauran nau’ikan tada kayar baya.

Ya ce “hakan ya zama dole domin irin wadannan rahotanni za su ba wa masu aikata ta’asa ayyukan da ba su dace ba da kuma ganin fifiko a ko da yaushe ko kuma a kullum, inda za su zama kanun labarai.”

Mista Kolo ya lura cewa Jihar da kasar, suna cikin mawuyacin hali, amma tare, “zamu iya cin nasara a wannan yakin. A matsayinmu na ’yan jarida kuma muna sa ido kan kare al’umma, mu ba jami’an tsaro hadin kai don kawar da fargabar talakawa tare da karfafa kwarin gwiwa ga jama’a”.

Dangane da karramawar, Mista Kolo ya ce an gudanar da taron ne domin karrama mutanen da suka bayar da gagarumar gudunmawa ga al’umma.

“A yau, mun hallara a nan ba wai don nuna murnar nasarorin da masu karramawar suka samu ba, a’a, mun kuma yi la’akari da dabi’un wadanda aka karrama suka nuna, kamar horo, tausayi da kishin daukakar rayuwar bil’adama.

Da yake bayyana wannan karimcin a matsayin wata hanya ta yabawa, karfafa gwiwa da kuma kalubalantar daidaikun mutane da su kara kaimi, Mista Kolo ya shawarci wadanda suka karrama da su dauki karramawar da aka ba su a matsayin wani abu na karamci domin kara jajircewa wajen yin fiye da haka.

Daga cikin wadanda aka karrama sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi limamin raya birane da karkara, Cif Anthony Hassan da ya yi fice a fannin bunkasa hakkin yan Adam musamman a fannin ilimi da Mista Jackson Ukuevo, Manajan Darakta na Ronchess.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here