Wanda Ya Gargadeka, Ya Gama Shiryaka: Damisa Ba Ta Canza Zanen Jikinta

0
436


Gaissuwa da fatan alkairi a gareku yan jarida.
Bayanai da suka iso ga kungiyar hadin kan matasan arewa shi ne kamfanin babbar matatar mai ta kasa a karkashin jagorancin Mallam Mele Kolo Kyari na shirye-shiryen mika kontiragin tsaron bututun matar mai zuwa ga makiyin kasa, dan fasa kwarin mai da fasa bututun mai da kuma sauran kayan aiki na gwamnati wai shi Oweizide Ekpemupolo wanda aka fi sani da Gwamnati Tompolo.
Wannan abin al’ajabi ne sosai, da hankali ba zai iya dauka ba a ce a matsayinmu na kasa, za mu dauki tilon hanyar samun kudin kasarmu, mu danka  amanar ta a hannun Tompolo, wanda ba a iya rabe sunan shi da fasa butun mai, satan mai, da barnar kayan gwamnati.
A matasyin mu na matasan arwar Nigeria, Tompolo daya yake da yan ta’adda kaman su Bello Turji, Nnamdi Kanu, Sunday Igboho, Muhammad Yusuf da sauransu, wa yanda basu daraja qasa, basu ganin komai illa watsewar Nigeria, rashin ladabi, da kuma rashin kunya ga Gwamnati me ci.
A matsayin mu na yan arewa wa yanda ke kula da gwamnati da harkokin gwamanti, a bisa yadda suka shafi yan qasa, baza mu tanqwashe hannuwan mu baa mu bari gwamnati tayi irin wannan gagarumin kuskuren danka bututun mata tar man mu a hannun wanda be dace ba, mara kishi qasa, mara tattali da adalci kuma makiyin ci gaban qasa.
Saboda haka, muna kira, muna roqo, muna kuma bada shawar ga kamfanin  babban matatar mai na qasa cewa su temaki bututun ma’adanan mu na man petur kar su miqa kwangila tsoron su zuwa ga Tompolo saboda ze gur bata tattali arzikin Nigeria.
Idan aka bashi wannan kwangilar, sauran yan ta’adda kaman su Bello turji, da Nnamdi Kanuda  zasu sa ran a basu kwangilar tsare fadar shugaban kasa, da iyalansa, da kuma shi kansa shugaban qasar.
Domin a nuna ma samari, manyan gobe cewa dogaro da kai, da neman na kai shi e yafi komai, ba shiga fituntunin zamani ba, da kuma sauran harkoki marasa kyau, kaman satar yanar gizo, da kingiyoyi na asirai dole ne a hana Tompolo wannan kwangilar, bama maganan bashi kwangila ba, dole ne a hana shi kusantar bututun mai na qasa baki daya.
Shawara kyauta ce, kuma ba a siyar da ita. Idan kunne yaji gangar jiki ya tsira.
Abdulsalam Mohammed Kazeem
Maitaimakin Kaakakin Kungiyar matasan Arewa

Leave a Reply