Watan Ramadan: Sanata Uba Sani Ya Taya Al’ummar Musulman Najeriya Murna

0
337

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SANATA mai wakiltar Shiyyar Kaduna ta tsakiya a zauren Majalisar Tarayya, Malam Uba Sani, ya bayyana cewa babban abin farin ciki ne a taya al’ummar Musulmi a fadin duniya murnar shiga watan Ramadan mai alfarma.

Sanatan wanda yake Dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, ya kara da cewa watan Ramadan na daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.

“Lokaci ne da ya kamata a yi amfani da muhimman dabi’u yadda ya kamata; Hakuri da kai, afuwa, sadaukarwa, nuna kauna kuma lokaci ne na taba rayuwar marasa galihu da masu rauni a cikin al’ummarmu ta hanyar ayyukan agaji.

“Ina kira gare mu da mu yi amfani da damar da muka samu a wannan wata na Ramadan wajen yin tunani kan matsalolin da kasarmu ke ciki, mu yi addu’a ga Allah Ya sa mu dace, mu ci gaba da zama a dunkule domin mu karya lagon abokan gaba da ke neman ruguza al’ummarmu.” Inji shi.

Sanata Uba, ya ci gaba da cewa watan Ramadan “lokaci ne na tunani, kamewa, sadaukarwa da addu’o’i ga Allah Madaukakin Sarki.”

“Babban makasudin wannan lokacin yana da ma’anarsa a gare mu shi ne domin samun mafita da kuma jagorancin Ubangiji daga kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu a cikin al’ummarmu.

“Ina yi wa ‘yan mazabata da al’ummar jihar Kaduna barka da azumin watan Ramadan mai alfarma, Allah ya sa ruhin wannan wata mai alfarma ya dawwama a cikin zuciyarmu, ya haskaka mana ranmu daga ciki”.

Leave a Reply