An Ga Watan Azumi A Najeriya – Sarkin Musulmi

0
436

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

BAYANAN da muke samu daga fadar Mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar III, ya tabbatar da ganin watan Ramadana mai alfarma a Najeriya wanda hakan ya tabbatar da cewa a gobe ne daya ga watan Ramadana don haka a gobe za a tashi da Azumin Ramadan.

Mai alfarma Sarkin musulmi ya bayyana Jihohin Kano, Borno, Sakkwato da sauran wadansu Jihohin ma da dama da aka ga watan Azumin.

Alhamdulillah! Mai alfarma Sarkin Musulmi ya baiyana ganin jinjiri watan Ramadan na wannan shekara 1443.AH.

Gobe ta kasance daya ga watan Azumi.
Allah Ya bamu ikon gabatar da ibada a cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here