Sojojin Sama Ne Za Su Dinga Raka Jirgin Ƙasa Na Kaduna-Abuja – Amaechi

1
732

Daga; Rabo Haladu.

GWAMNATIN Najeriya ta ce daga yanzu jiragen sama ne za su dinga yi wa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna rakiya da zarar ya ci gaba da aiki.

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara Jihar don gane wa idonsa abin da ya faru bayan harin da ‘yan fashi suka kai kan jirgin a ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum takwas.

Bayan ya duba waɗanda suka jikkata a Asibitin 44 na Sojoji a Kaduna, Mista Amaechi ya kuma gana da Hafsan Sojojin Sama Air Marshal IO Amao da kuma Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.

“Na faɗa wa hafsan sojan sama cewa idan muka gama gyaran layin dogo, jirgin zai ci gaba da aiki bisa rakiyar tsaro ta sama daga sojan sama har sai an saka kayayyakin tsaro daga nesa kamar yadda shugaban ƙasa ya ba da umarni,” in ji Amaechi cikin wani saƙon Tuwita.

Ministan ya zargi “abokan aikinsa” cewa su ne ke hana ruwa gudu tun lokacin da ma’aikatarsa ta nemi kuɗin sayen kyamarorin tsaron a baya

1 COMMENT

Leave a Reply