An Kammala Taron Kaddamar Da Shugabannin Jam’iyyar APC Lafiya A Kano Ta Arewa

0
404

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AN gudanar da taron Kaddamar da Shugabannin Jam’iyyar APC na shiyyar Kano ta arewa mai kunshe da yankunan kananan hukumomi 13 cikin nasara tare da jaddada bukatar ganin Jam’iyyar ta APC ta sake lashe zabukan Shekara ta 2023 da babban rinjaye.

Wakilin mu wanda ya zagaya harabar wajen taron ya ruwaito cewa dukkanin shugabannin Jam’iyyar APC na wannan shiyya sun halarci taron Kaddamar da su bisa jagorancin shugabannin kananan hukumomin dake shiyyar da sauran masu ruwa da tsaki.

Sannan an gudanar da taro bisa la’akari da yanayi na karatowar zabukan Shekara ta 2023 da kuma kokarin bin ka’idojin uwar Jam’iyya ta kasa da kuma tabbatar da cewa an bi tsarin jadawali da sharuddan hukumar zabe mai zaman kanta wato (INEC) da kuma yadda babban taron Jam’iyyar na kasa yake Kara matsowa.

A jawabin sa, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa APC a Jihar Kano daya ce, sannan kowa yana da damar kasancewa dan Jam’iyyar domin a hada hannu wajen ganin ita ce ta sake lashe zabukan Shekara ta 2023 a duka matakai daban-daban duba da yadda take da kyawawan manufofi.

Gwamna Ganduje ya kuma bayyana cewa APC zata ci gaba da gudanar da shugabanci nagari a mataki na kasa da Jihohi da kuma kananan hukumomin kasarnan ta yadda kowane dan kasa zai amfani zaben da ya yi kamar yadda ake gani a kowace Jiha da take mulki.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun sanar da cewa bisa yadda aka gudanar da wannan taro na shiyyar Kano ta arewa, ko shakka babu APC tana da dumbin magoya baya a kasa kuma ita ce Jam’iyya da al’umma suke goyon baya a Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here