ABG Ya Raba Motoci Da Babura Ga Shugabannin Jam’iyyar PDP A Kaduna Ta Arewa

0
640

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON dan majalisar tarayya, Honarabul Shehu Bawa wanda aka fi sani da ABG ya nuna halin karamci ga wasu manya da kananan ‘ya’yan jam’iyyar PDP ta hanyar bayar da motoci da babura ga wasu mambobin Jam’iyyar kyauta a fadin mazabar Kaduna ta Arewa.

ABG ya kara da cewa ganin irin yadda wasu ke biyayya ga jam’iyyar ne yasa ya kudiri aniyar yi musu wannan kyautar don rage radadin kuncin rayuwa, domin a cewar dan majalisar, hakan ne zai sanya shi cikin kwanciyar hankali, ganin al’ummar mazabar sa na bukatar kayayyakin more rayuwa da sauran ababen more rayuwa.

Da yake mika makullan motoci iri-iri da babura ga wadanda suka ci gajiyar babban taron, Daraktan yakin neman zaben na ABG, Alhaji Ibrahim Siraj ya bayyana cewa an zabo shugabannin Unguwanni da sauran Jami’an Jam’iyyar a Kaduna ta Arewa don gudanar da kyaututtukan domin saukaka ayyukansu a zaben 2023 da zai gudana wanda hakan ke tabbatar da jam’iyyar PDP za ta yi nasara da gagarumin rinjaye.

Siraj, ya bayyana cewa an baiwa shuwagabannin jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar motoci 20 da babura 20, inda ya kara da cewa sama da matasa da mata 2000 daga Kaduna ta Arewa an horar da su sana’o’i daban-daban daga dan majalisar.

Ya ce wasu mutane 500 ne suka ci gajiyar kiwon kaji da kifi, yayin da wasu da aka horas da su kan fasahohin noman shinkafa da hatsi kuma an ba su injinan niƙa da kudi naira dubu ashirin kowannensu domin su fara kasuwanci.

Ya kara da cewa Honarabul ABG dai ya kasance yana gina jama’a da tsare-tsare na jam’iyyar a fadin Jihar, wanda hakan ya sa ta zama kakkarfa, da karfin da zai iya kwace gidan Sir Kashim Ibrahim daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a 2023.

Siraj ya tabbatarwa da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ba a saka su a cikin sabuwar kyautar mota da babura cewa nasu na kan hanya, inda ya bukace su da su yi hakuri su yi aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023.

Shugabar Mata ta PDP ta Kaduna ta Arewa, Hajiya Bilkisu wadda ta yi magana a madadin wadanda suka ci gajiyar shirin ta yaba wa ABG bisa wannan karamcin, inda ta bayyana dan siyasar a matsayin mutum mai gaskiya, mai tausayi kuma mai karamci wanda gudummawar da hidimar jam’iyyar za ta dade a ciki.

Leave a Reply