Soshiyal Midiya:Yadda Alheri Yake Nema Ya Zama Mugunta

0
1179

Daga Musa Muhammad Kutama

KAFAR sada zumunta wadda jama’a d da damar gaske ke farin cikin damuwar ta saboda dalilai na sada zumumci ga ‘yan uwa na kusa da na nesa bayan wannan ma soshiyal midiya ta zama wata kafa ce ga ‘yan kasuwa ta tallata hajarsu ga mubakata .

Tun daga lokacin da iskar sauyin zamani da ci gaban sa ya samu kusan shekaru 20 koma fiye da haka a Najeriya sannu a hankali an dada samun karin wasu shafukan sada zumunta bayan facebook,an samu To Go ,an samu Whatsapp sauran su ne twitter da instagram bugu da kari tiktok da telegram da sauran wadanda ba’a ambata ba.

Yadda wasu jama’a suke cin gajiyar soshiyal midiya, mutane ‘yan kasuwa da masu shirin fina-finai sun dade suna cin gajiyar kafar you tube wadda hatta wasu mutane kan bude Telbijin a youtube da sauran su .

Akwai kafagen yada labarai narkatai a soshiyal midiya dake wallafa labarai wasu masu wallafa irin wadannan labarai kan bi kaida da Kuma dokar aikin yada labarai wasu ko oho .

Illar soshiyal midiya ga Al’umma :kowane abu yana da ingantacce wani kuma ana samun baragurbi ina nufin soshiyal midiya illar da kafar tiktok take yi wa al’umma ya fi gaban a kira su kafa ce wadda wasu mutane maza da mara suka mayar wajen yada badala ko kuma nauikan takadarci kamar yadda ake zargin su.wannanan nema ya sanya wasu masu shirya fina-finan Hausa suke ankarar da al’umma irin illolin wadancan kafagen sada zumunta (tiktok) da makamantan su wajen cin zarafin ‘ya’ya mata da ake yi ana amfani da daukar bidiyon mace a yi mata barazanar bata mata suna .

A wannan yanayi akwai bukatar iyaye,malaman addini su tashi tsaye wajen yiwa ‘ya:ya da al’umma fadakarwa a kan illolin  da wasu daga cikin kafagen sada zumunta ke yi wa al’umma 

Allah shiryemu baki daya.

Musa Muhammad Kutama

Tsohon wakilin radio France international na farko a yankin Niger Delta ya rubuto daga Kalaba jihar Kuros Riba

Leave a Reply