Muna Kokarin Bunkasa Harkokin Kasuwancin Zamani Ne Tsakanin Najeriya Da Chadi – Ambasada Abubakar

0
445

…Ya Yi Shuru Game Da Batun Ko Zai Tsaya Takarar Gwamna

Dag; Mustapha Imrana Abdullahi.

JAKADAN Najeriya a kasar Chadi kuma tsohon shugaban rundunar sojojin Saman Najeriya Mashal Sadiq Baba Abubakar mai ritaya ya ce ya halarci kasuwar duniyar kasa da kasa ne da ke ci a Kaduna domin kokarin ganin an bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da kasar Chadi.

Sadiq Baba Abubakar, ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a harabar kasuwar, jim kadan bayan kammala taron bude kasuwar da wakilin shugaban kasa ya yi a ranar Asabar, amma dai yaki amsa tambayar manema labarai a game da rade- radin da ake yi cewa wai ya na son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi.

Sai ya ce “mun zo nan ne domin maganar kasuwar duniya”.

Tsohon shugaban rundunar sojan Saman, wanda kuma a yanzu shi ne jakadan Najeriya a kasar Chadi, ya ce ya zo da wata tawaga ce ta yan kasuwa daga kasar Chadi domin tattaunawa a kan irin abubuwan kasuwancin da ya dace kasashen biyu su tattauna a kansu, inda ya tabbatar da cewa samun irin wannan damar zai sama wa kasashen biyu damar bunkasa harkokin kasuwanci a tsakaninsu.

Kamar yadda ya ce, “hakika a halin yanzu al’amari ne mai zaburarwa yadda duniya take gogoriyon ganin sun magance duk wani kalubale na gasa a batun ci gaba, don haka ne ma nake ganin taken kasuwar na Bana ya da ce.

“Duk lamari ne na ganin an kara zage damtse domin ganin tattalin arzikin Najeriya ya shiga jerin gogoriyon da kasashen duniya ke yi don ana bukatar hakan”.

“Don haka wannan rana mai matukar muhimmanci ce, saboda haka nake yaba wa wadanda suka shirya wannan kasuwa, wato cibiyar bunkasa harkokin kasuwanci ta Kaduna kuma ina saran za su leka sauran bangarori ma da nufin cin ribar da ke wurin, kuma zamu ga irin yadda za mu fadakar da jama’a su zama sun samo suna tare da tsarin

“Wannan shiri ne mai kyau, ..don haka kamar yadda na ce ne mun zo da tawaga daga kasar Chadi, wadanda suke da zimma domin sun ga akwai dama da yawa a nan. Muna fatan za su samu cikakkiyar damar cin moriyar abin da suke gani a nan”.

“Duk irin kokari da Zimmar da suke da ita, hakika zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu wato Najeriya da Chadi”, inji Sadiq Baba Abubakar.

Da yake ci gaba da yi wa manema labarai jawabi kuma, Ambasadan ya ce a cikin harshen Hausa cewa “abu ne mai matukar farin ciki”.

“Wannan ne na farko da muka samu zuwa da wata tawaga daga kasar Chadi domin ganewa idanunsu abubuwan da za su amfani al’ummar kasarsu”.

“Kuma muna son mu gayyaci yan Najeriya zuwa Chadi domin suma su ga wadancan abubuwan da za su amfani jama’ar Najeriya, hakika wannan damace mai matukar muhimmanci.

Lokacin da aka yi masa tambaya a game da batun ko zai tsaya takara, sai ya ce ..”A’a …ai wannan batun kasuwar duniya ne muke yi kawai”.

Leave a Reply