Za A Fara Aikin Gina Kasuwar Hatsi Ta Zamani A Garin Saminaka

0
389

Daga; Isah Ahmed, Jos.

SHIRYE – shiryen gina babbar Kasuwar hatsi ta zamani da Gwamnatin Jihar Kaduna take son ta yi, a garin Saminaka ya kankama. Tuni Karamar Hukumar Lere ta baiwa ‘yan kasuwar da suke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar wa’adin nan da makonni biyu, su kwashe kayayyakinsu daga kasuwar su koma babbar tashar mota ta garin Saminaka, don baiwa kamfanin da zai gudanar da wannan aiki wuri.

Wata takarda da Karamar Hukumar ta rubutawa Sarkin Kasuwar hatsi ta Saminaka, Manu Isah Idris wadda ke dauke da sanya hanun, Daraktan gudanarwa na Karamar Hukumar, Saleh Ahmed Kargi ta baiwa ‘yan kasuwar wa’adin nan da mako biyu su kwashe kayansu don a fara wannan aiki.

Da yake zantawa da wakilinmu, kan wannan aikin gina kasuwar hatsi ta zamani a garin Saminaka, Sarkin Kasuwar hatsi ta Saminaka Manu Isah Idris, ya bayyana matukar farin cikinsa.

Ya ce wannan sabuwar kasuwa, kamar yadda aka tsara za ayi ta, zata yi fice a dukkan kasashen Afrika, saboda shaharar da wannan yanki ya yi, a harkokin noma.

“Wannan kasuwar hatsi kashi 75 na yan hatsi ne, sauran kashi 25 kuma za a gina bangaren mahauta da tashar mota da yan katako da yan tireda da banki da ofishin yan sanda da ofishin kashe gobara da kuma wuraren ibada”.

Leave a Reply