Hukumar NNDC Ta Amince Da Raba Naira Miliyan 125 Na Tsabar Kudi Da Hannun Jari

0
386

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A TARON shekara-shekara na Kamfanin Ci gaban Kasa na New Nigeria Development Company (NNDC) da aka kammala kasafin kudi na shekarar da ya kare a ranar 31 ga Maris, 2021, masu hannun jari sun amince da raba ribar kudaden da aka samu na Naira miliyan 100 (daidai da kobo 20 a kowace kaso). Taron ta kuma amince da raba naira miliyan 25 na kudaden alawus-alawus, kwatankwacin kaso 1 na bonus ga kowane hannun Jari 20 da masu hannun jarin NNDC ke da shi.

Bugu da kari, kungiyar ta amince da ware Naira miliyan 15 kowannensu ga shirin bunkasa sana’o’i na matasa da kuma cibiyar ilmantarwa ta Musa Bello.

Shugaban Kamfanin, Tanimu Yakubu ne ya sanar da amincewar masu hannun jari a lokacin da yake gabatar da bayanan kudi na kamfanin na shekarar da ta kare a ranar 31 ga Maris, 2021 a yayin babban taron shekara-shekara karo na 53 da aka gudanar a ranar Juma’a, 11 ga Fabrairu, 2022.

Da yake tsokaci kan ci gaban da kamfanin ya samu a cikin shekarar da ake bitar, Shugaban Kamfanin, Tanimu Yakubu ya bayyana cewa, kasuwar ta tsaya a kan Naira miliyan 629.15 idan aka kwatanta da daidai lokacin da aka samu Naira miliyan 625.58 wanda ya nuna an samu karin Naira miliyan 5.57 ko kuma 0.98. %. Kudaden aiki na tsawon lokacin da ake bitar ya kai Naira miliyan 541.99 sabanin adadin shekarar da ta gabata na Naira miliyan 589.91 wanda ya bayar da kyakykyawan bambancin Naira miliyan 47.92 ko kuma kashi 8.8%. Ribar kafin haraji na shekarar da ta kare a ranar 31 ga Maris, 2021 ta tsaya a kan Naira miliyan 335.42 a daidai lokacin da ake biyan harajin da ya kai Naira miliyan 273.22.

Yakubu ya bayyana cewa, kamfanin ya ci gaba da gudanar da harkokin zuba jari a cikin abokansa sannan ya ambato kamfanoni da nufin inganta yadda ake dawo da su yayin da suke bin ingantacciyar dabarar gudanarwa ga kamfanonin na kasa. Ya kara da cewa, adadin kudin da NNDC ta zuba ya kai Naira miliyan 692.14 sabanin yadda aka hada kasuwarsu ta N10.61 biliyan a ranar 31 ga Maris, 2021.

Ya kuma bayyana cewa kudaden masu hannun jari sun tsaya a kan N19.21 biliyan a ranar 31 ga Maris 2021.

A kan Bunkasa, Shugaban ya ce, Kamfanin ya ci gaba da tallafawa shirin bunkasa wutar lantarki na (YPDS) da kuma rahotani na musamman wato Students Special Project (SSP) inda ake horar da daliban da suka kammala karatu daga Arewacin Najeriya zuwa zama Chartered Accountants, Chartered Insurers, Stock Dill da IT Specialist.

Ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu NNDC na da kwararru 1438, a wadannan fannonin a cibiyoyin Kaduna, Kano, Ilorin da Gombe, tare da hadin gwiwar Abokin huldar su wato Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN).

Dangane da hangen nesa na kamfanin nan gaba, Shugaban Hukumar, ya ce, “Muna da kwarin gwiwa game da shekarar kudi ta gaba saboda ana sa ran cewa manufofin gwamnati daban-daban za su fara yin tasiri mai kyau ga yanayin kasuwanci”.

Ya ce NNDC za ta ci gaba da himma wajen aiwatar da ayyuka daban-daban da Kamfanin ya samar, tare da cin gajiyar sabbin hanyoyin kasuwanci da nufin inganta kudaden da Kamfanin ke samu. NNDC na sa ran duka abokan tarayya na gida da na waje za su taka rawar gani a wannan fanni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here