Kasuwancin Hadin Gwiwa Na Bunkasa Tattalin Arziki – Sarkin Zazzau

1
358

Mustapha Imrana Abdullahi

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli,ya bayuana cewa tsarin kasuwancin hadin Gwiwa na kara bunkasa dukkan harkokin kasuwanci da kuma samun karko a koda yaushe.

Sarkin Zazzau ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a masaukin baki na Shagalinku da ke Sakaru, karamar hukumar Soba.

Mai martaban ya kara da cewa “idan ana son a samu nasara a dukkan kasuwanci dole ne a samu shawarar kwararru na musamman wajen bayar da shawara da kuma ba da umarni ta yadda za a samu ci gaban da kowa yake bukata.

Sarkin Zazzau ya yi kira ga dukkan masu gudanar da harkokin kasuwanci a masarautarsa da su hanzarta samar da ingantaccen tsari domin a samu yin hadin Gwiwa da masarautar da nufin samar da ci gaba.

Saboda haka ya yabawa Alhaji Umaru Shagalinku a bisa irin yadda ya mayar da Zariya wajen bunkasa harkokin kasuwanci sai ya shawarce shi ya canza harkarsa ta kasuwanci ya zuwa wani yanayin samar da riba mai yawa da za ta samar da kudi.

Tun da farko a jawabinsa, Alhaji Umatu Shagalinku ya amince da shawarwarin na Sarkin Zazzau a game yadda harkokin kasuwanci za su bunkasa sosai.

Umar Shagalinku ya kuma bayyana farin cikinsa da ziyarar mai martaba Sarkin Zazzau, ya bayyana ziyarar da cewa wani al’amari ne mai matukar muhimmanci kwarai.

1 COMMENT

Leave a Reply