Yan Bindiga sun buɗewa tawagar motocin Sanata Ifeanyi Ubah wuta

0
280

Yan Bindiga sun buɗewa tawagar motocin Sanata Ifeanyi Ubah wuta a garin Enugwu-Ukwu dake ƙaramar hukumar Njikoka dake jihar Anambra ranar Lahadi.

Majiyoyi sun bayyana cewa ana hasashen kimanin yan sandan shida aka kashe a musayar wutar, rahoton Punch.

Wata majiya ta bayyana cewa: “Wasu ɓata gari sun kaiwa Sanata Ifenyi Ubah hari a Enugwu Ukwu. Wannan shiryayyen hari ne. Kwantan ɓauna sukayi masa.”

Leave a Reply