Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
AN bayyana shekarar 2023 a matsayin wata shekara da za ta zama ta Ketare siradi a matsayin Najeriya.
Dan takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyyar PDP Muhammad Hayatu-deen, ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa yayan Jam’iyyar bayanin dalilinsa na tsayawa takara.
“Hakika babban dalilin tsayawa takara shi ne saboda yadda Najeriya ta samu kanta a lamarin tsaro ne, kasancewar batun tsaro akwai abubuwa da dama da suke tattare da shi. Misali akwai tsaro kan tattalin arziki, tsaro kan lamuran siyasa da kuma tsaro a kan harkokin jama’a, duk da ya kasu kashi kashi da tsaron tattalin arziki ne ya haifar da wadannan matsalolin don haka idan na zama shugaban kasa zan yi iyakar bakin kokari na domin warware matsalar”, inji Hayatu-deen.
Da yake amsa tambayar manema labarai a game da batun yin sasanci a tsakanin yan takarar shugaban kasa na PDP kuwa, cewa ya yi ” ai wani al’amari ne da muka bari domin kashin kan mu a tsakanin yan takara, don haka za mu iya komawa nan gaba kafin lokacin zaben shugaban da zai tsayawa PDP takara a iya yin hadaka a tsakanin yan takara”.
“Ya dace mutane masu zaben dan takara su tsaya tsaf su duba da hankalinsu wa ya dace su zaba a matsayin dan takara, ni dai ina da dimbin kwarewa kuma zan yi abin da ya dace wajen ganin Najeriya ta ci gaba a dukkan fannonin rayuwa baki daya”.
“Hakika shekarar 2023 wata shekara ce da kowa ya zama ya duba ta sosai domin wani al’amari ne na batun Ketare siradi ko za mu ci gaba da zama dunkulalliya ko kuma yaya lamarin zai kasance?
Kamar yadda wasu da yawa suka sanni na gudanar da rayuwa ta wajen yin aiki a Jihar Kaduna don haka ni ba Bako ba ne a nan kuma ina da tarihin samun nasara kwarai.
Da yake tofa albarkacin bakinsa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, bayyana Mohammed Hayatu- deen ya yi a matsayin kwararren mutum a fannin tattalin arziki da harkar Banki da kuma sauran fannoni daban daban na inganta rayuwar dan Adam.
“Mutum ne da ya gudanar da mafi yawan rayuwarsa a nan Kaduna don haka sanannen mutum ne da aka san abin da zai iya yi idan ya zama shugaban kasa”.
Shima shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna Mista Felix Hassan Hyat bayan ya yi maraba da zuwan dan takarar tare da tawagarsa, ya lissafa irin yawan masu zaben dan takara da suke da shi a Jihar Kaduna inda ya ce a yanzu su na da mutane 78 kuma nan da yan kwanaki yawansu zai wuce dari domin akwai wasu Shari’u a kotu da suke saran samun nasara da zai taimaka masu samun karin yawan deliget da hakan zai kara bunkasa karfin Jihar Kaduna idan an je zaben dan takarar shugaban kasa a wajen babban taron da za a yi a garin Abuja hedikwatar tarayyar Najeriya.
“Mu na da kwararan masu zaben dan takara mutum biyu, daya tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Muhammadu Namadi Sambo da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Ahmad Muhammad Makarfi don haka Jihar Kaduna ta zama gagarabadau a dukkan fanni”.