Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
MATAIMAKIN shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa dalilin da ya sa yake son zama shugaban kasar Najeriya shi ne domin ciyar da kasar gaba.
Osibaji, ya bayyana haka ne a daren jiya Lahadi yayin da yake neman goyon bayan wakilan APC na Kaduna.
Mataimakin shugaban kasar wanda ya gana da wakilan jam’iyyar a sirrance, ya isa dakin taro na dandalin Murtala da misalin karfe 7:36 na yamma tare da gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-rufai da sauran manyan jami’an gwamnati.
Osinbajo ya ce, idan aka zabe shi a matsayin dan kasa na daya, ba zai dauki lokaci mai tsawo yana nazarin yadda ake gudanar da mulki ba tun da ya saba da tsarin ba kamar sauran ba.
Ya kuma bayyana cewa da gogewarsa ta shekaru bakwai a harkokin mulki, zai taka rawar gani a ranar farko ta mulki idan ya zama shugaban kasa a 2023.
A cewarsa, akwai bukatar a baiwa ilimi fifiko a kasar, yayin da ya kuma kara da cewa dole ne a samu sauyi kuma dole ne Najeriya ta fara gudanar da ilimin ta yanar gizo, kamar yadda ya ce kudaden da ake ba su a fannin ilimi bai wadatar ba kuma akwai bukatar kyautatawa.
A fannin noma, Osinbajo ya ce akwai bukatar a rarraba ma’aikatar noma ta yadda tsarin noma zai yi aiki yadda ya kamata tare da mai da hankali kan abubuwan more rayuwa da sauran fannoni.
Ya kuma jaddada bukatar samar da tsarin da zai magance rikice-rikice nan take, a matsayin hanyar magance kalubalen zamantakewa, yayin da ya ce dole ne a samar da tsarin zamantakewa wanda zai magance kalubalen kowa.
Da yake magana game da faduwar darajar Naira a halin yanzu, ya ce kasar ce ta tsara yadda za a yi, kuma mafita mafi kyau ita ce a bar kasuwa ta tantance adadin kudin.
“Lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika min mulki gabanin ziyarar da ya kai Landan, na tambayi shugaban kasa ko zan kawo masa rahoto kai tsaye, amma shugaban ya amsa da cewa ya amince.
“Kuma a ziyarar da shugaban kasa ya kai Landan, na samu damar halartar wasu harkoki masu sarkakiya da mahimmanci wadanda suka nuna karfina na ciyar da kasar gaba,” Osinbajo ya bayyana.