Connect with us

Al'ajabi

Ɗan Majalisar da ya faɗi a taron Tinubu a Jos ya rasu

Published

on

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Mushin II a majalisar dokokin jihar Legas, Sobur Olayiwola Olawale Wanda aka fi sani da Omititi ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi a lokacin da ake tsaka da ƙaddamar da yaƙin neman zaben ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata a garin Jos na jihar Filato.

Omititi na cikin ‘yan siyasar da suka hallara a garin Jos domin ƙaddamar da yaƙin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya faɗi a wajen taron kuma ya rasu bayan wasu ‘yan mintuna da faɗuwarsa.

Wani jigo a jam’iyyar APC da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa suna tare da Olawale tun ƙarshen makon daya gabata.

“Mun haɗu ne a gidan Sanata Ganiyu Olanrewaju Solomon a ranar Lahadi inda muka sha hira, garau yake cikin koshin lafiya.

“Ba tare da fitowar binciken abinda ya kashe shi ba, muna ganin zai iya zama hawan jini.

“Koma dai meye ya haifar da mutuwarsa, mutuwarsa ta razana mu kuma abin baƙin ciki ne” inji shi.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Ɗan takarar Gwamnan PDP a Abia ya rasu | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Al'ajabi

An ƙona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Published

on

An ƙona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta yayin da mutane ke Sallar Asuba ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Gadan da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar ta Kano, da misalin karfe 5:20 lokacin da ake sallah, a cewar sanarwa ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa da TRT Afrika Hausa faruwar lamarin da kama mutumin da ake zargi, sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Abdullahi Kiyawa ya ce bincike ya nuna cewa mutumin da ake zargi da cinna wutar Shafi’u Abubakar mai kimanin shekaru 38 ya jefa wata roba ne ɗauke da fetur cikin masallacin, sannan ya cinna wuta.

KU KUMA KARANTA: Mahara a Anambara sun ƙona fadar babban Basarake ƙurmus

Kakakin ‘yan sandan ya ce mutum 24 ne suka ƙone a masallacin, da suka haɗar da manya 20, yara huɗu.

An garzaya da duka waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don ba su kulawa, amma babu wanda ya mutu a haɗarin, a cewar sanarwar ‘yan sandan.

Continue Reading

Al'ajabi

An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano

Published

on

An tsinci gawar wata ɗaliba mai suna Aisha Yahaya ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil, a wani gida da ke wajen jami’ar.

Aisha, ɗaliba ce da ke matakin karatu na uku wato ‘level 300’ a sashen nazarin Kimiyya da Fasahar Abinci na jami’ar wadda aka tsinci gawarta bayan ta koma ɗakinta.

An ce ɗalibar ta rubuta jarrabawarta ta farko a zangon karatun na farko da ake yi a jami’ar.

Wasu daga cikin abokan karatunta sun danganta mutuwarta da shiga cikin matsi da damuwa a dalilin karatu da kuma zana jarrabawar.

A cikin wasiƙar ta’aziyyar, hukumar jami’ar ta bayyana matuƙar baƙin cikinta dangane da rasuwar Aisha Yahaya.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar wani mutum a kan titi a Kano

Sanarwar ta ce, “Aisha ɗaliba ce mai hazaƙa wadda ta rasu a dalilin bugun zuciya. Za a riƙa tunawa da ita a kan sha’awarta na karatu da jajircewarta kan harkokin karatunta.”

Jami’ar ta ƙara da cewa, ba a iya gano wata da ke tattare da ita ba gabanin mutuwarta saboda ba ta nuna alamun rashin lafiya ko fama da wata cuta ba.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like