Ɗalibin sakandare a Benuwe ya kashe kansa

0
341

Wani ɗalibin makarantar sakandire mai shekaru 17 mai suna Terhemba Tyochivir ya kashe kansa a Akpehe da ke wajen birnin Makurɗi a jihar Benuwe.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe, SP. Catherine Anene, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Makurɗi ranar Juma’a.

An ce Tyochivir ɗalibi ne a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Gboko, har zuwa ranar Alhamis da ya kashe kansa.

Sai dai ba a fayyace cikakken bayani game da wannan musiba da aka samu a ofishin ‘yan sanda na E Division da ke Makurdi ba.

KU KUMA KARANTA: Matashi ɗan shekara 17 ya kashe kansa a Bauchi

Shaidu sun ce marigayi Tyochivir bayan an gano shi ba shi da rai, an garzaya da shi asibitin Bishop Murray na Makurɗi, inda ƙwararrun likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

A halin da ake ciki, yunƙurin yin magana da mahaifin marigayin, Kula Tyochivir, bai yi nasara ba kamar yadda ya yi alƙawarin yin magana a wani lokaci.

Leave a Reply