Ɓangarorin da ke gaba da juna a Sudan sun amince da tsagaita buɗe wuta na kwanaki uku da za a fara daga tsakar daren ranar Talata, yayin da ƙasashe da dama ke fafatukar kwashe ‘yan ƙasar su daga ƙasar da ke fama da rikici a Afirka.
“Bayan zazzafar tattaunawar da aka yi cikin sa’o’i 48 da suka gabata, Rundunar Sojin Sudan (SAF) da Dakarun Ba da Agajin Gaggawa (RSF) sun amince da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a faɗin ƙasar daga tsakar dare a ranar 24 ga Afrilu, wadda za ta ɗauki tsawon sa’o’i 72,” in ji sakataren harkokin wajen Amurka.
KU KUMA KARANTA: Hukumar NEMA ta jaddada ƙudirinta na kwashe ‘yan Najeriya da suka maƙale a Sudan
Antony Blinken ya faɗa a ranar Litinin a wata rubutacciyar sanarwa. Yunƙurin tsagaita wutar da aka yi a baya bai ci nasara ba, yayin da ƙazamin faɗan da aka shiga mako na biyu ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 427 tare da jikkata sama da 3,700 a cewar hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sa’o’i kaɗan kafin sanarwar Blinken, Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi gargaɗin cewa tashin hankalin “yana da haɗari ga wani mummunan tashin hankali a Sudan wanda zai iya mamaye yankin baki ɗaya.” Sai dai ya yi ƙira ga membobin kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da su yi iya bakin ƙoƙarinsu.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, RSF ta ce ta amince da tsagaita wutar “domin buɗe hanyoyin jin ƙai, da sauƙaƙa zirga-zirgar ‘yan ƙasa da mazauna.
“Haka kuma don ba su damar biyan buƙatunsu, isa asibitoci da wuraren tsaro, da kuma kwashe ofisoshin diflomasiyya.” A ƙarshen mako, ƙasashe sun kwashe jami’an diflomasiyyarsu da ‘yan ƙasarsu, yayin da faɗa ya ɓarke a sassan babban birnin ƙasar mai yawan jama’a.
Taƙaitaccen kwanciyar hankali a rikicin ya baiwa fararen hula ‘yan ƙasashen waje tserewa daga Sudan zuwa tsira.
Tsagaita wuta na kwanaki uku na yanzu, idan har ta ɗore, na iya samar da damar isar da muhimman albarkatu kamar abinci da magunguna ga masu buƙata.
[…] KU KUMA KARANTA: Ɓangarorin da ke gaba da juna a Sudan sun amince da tsagaita buɗe wuta […]
[…] KU KUMA KARANTA: Ɓangarorin da ke gaba da juna a Sudan sun amince da tsagaita buɗe wuta […]