Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Mushin II a majalisar dokokin jihar Legas, Sobur Olayiwola Olawale Wanda aka fi sani da Omititi ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi a lokacin da ake tsaka da ƙaddamar da yaƙin neman zaben ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata a garin Jos na jihar Filato.
Omititi na cikin ‘yan siyasar da suka hallara a garin Jos domin ƙaddamar da yaƙin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya faɗi a wajen taron kuma ya rasu bayan wasu ‘yan mintuna da faɗuwarsa.
Wani jigo a jam’iyyar APC da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa suna tare da Olawale tun ƙarshen makon daya gabata.
“Mun haɗu ne a gidan Sanata Ganiyu Olanrewaju Solomon a ranar Lahadi inda muka sha hira, garau yake cikin koshin lafiya.
“Ba tare da fitowar binciken abinda ya kashe shi ba, muna ganin zai iya zama hawan jini.
“Koma dai meye ya haifar da mutuwarsa, mutuwarsa ta razana mu kuma abin baƙin ciki ne” inji shi.
[…] KU KUMA KARANTA:Ɗan Majalisar da ya faɗi a taron Tinubu a Jos ya rasu […]