Ƙungiyar lauyoyi ta bayyana damuwa kan tauye ‘yancin ba da kariya

0
101

A jamhuriyar Nijar, ƙungiyar lauyoyi ta zargi hukumar yaƙi da mahandama ta COLDDEF da tauye wa wasu ƙusoshin hamɓararriyar gwamnati da ta ke gudanar da bincike akansu damar cin moriyar ‘yancin samun kariya kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada.

A lokacin da yake gabatar da sanarwar a gaban ɗaukancin lauyoyin ƙasar, shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Barreau des Avocats du Niger, Batonnier Kadri Oumarou, ya bayyana irin tarnaƙin da suke zargin hukumar yaƙi da cin hanci ta COLDDEF na yi wa ayyukansu, a yunƙurin kare wasu jiga-jigan gwamnatin da sojoji suka kifar da ake tuhuma da rub-da ciki akan dukiyar ƙasa.

Ƙungiyar na mai tunatar da hukumomin mulkin soja matsayin samun kariya a jerin ‘yancin da dokokin cikin gida da na ƙasa da ƙasa suka yi tanadi ga kowane mutum a matsayinsa na ɗan’Adam.

Yunƙurin ankarar da shugabanin harkokin shara’a irin illolin da ke tattare da wannan ƙulli ya ci tura, inji lauyoyin.

KU KUMA KARANTA:An cafke lauya kan lakaɗa wa matarsa duka

Ƙungiyar na mai mamakin yadda hukumar COLDDEF ke mursisi kan ‘yancin ba da kariya, alhali abu ne da hukumomin mulkin soja da kansu suka yi amanna da shi.

Muryar Amurka ta tuntuɓi kakakin COLDDEF Son Allah Dambaji, domin jin martanin da hukumar za ta mayar, sai dai ya faɗi cewa suna shirin gudanar da taro kan wannan batu, a halin yanzu ba zai iya cewa kala ba, saboda haka a jira idan komai ya kammala za a ji daga gare su.

Wannan kace-nace game da tsarin aikin na hukumar da gwamnatin mulkin sojan Nijer ta kafa na wakana ne a wani lokaci da wasu ‘yan ƙasa ke zarginta da jinkiri wajen tatso kudaden da ake hasashen an wawure a shekarun baya.

Leave a Reply