Ƙungiyar dattawan arewa ta yi watsi da amincewar Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa

0
329

Ƙungiyar dattawan Arewa, (ACF), ta nesanta kanta daga amincewar Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa da haɗin gwiwar ƙungiyoyin Arewa suka yi.

Musa Saidu, memba a ƙungiyar ACF ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja. Saidu, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar Arewa mazauna Kudancin Najeriya, ya ce amincewa da Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa zai haifar da halaka ga Arewacin Najeriya.

“Don haka muna nesanta kanmu daga amincewa da Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa da gamayyar ƙungiyoyin Arewa suka yi. “ƙungiyar gamayyar ba ta yi wa Arewa magana ba, tana magana ne da kanta.

“Ba wata ƙungiyar Arewa ta gaskiya da za ta so amincewa da Akpabio a kan wani muhimmin matsayi irin na Shugaban Majalisar Dattawa saboda ba shi da alaƙa da Arewa.

KU KUMA KARANTA: Kotun ƙoli ta bayyana shugaban majalisar dattawa, Lawal a matsayin ɗan takarar sanatan Yobe ta Arewa

“Mu ne mutanen da suka san Akpabio, saboda mu mazauna Kudu ne, mun san waɗanda ke son mutanen Arewa kuma Akpabio ba ya cikin su,” inji shi. Saidu ya ƙara da cewa tabbas ƙungiyar ta amince da hakan ne bisa jahilci.

“Ina so in yi Allah wadai da amincewar da aka yi a cikinta saboda an yi shi ne bisa jahilci. “Har ila yau, mai yiyuwa ne an bai wa ƙungiyoyin wasu ƙwarin gwiwar amincewa da Akpabio.

“Ina so in ce ’yan Arewa ba mabarata ba ne da za su goyi bayan mutanen da ba su da alaƙa da su saboda jawo hankalinsu,” inji shi. Saidu ya ce ƙungiyar ACF za ta ci gaba da fafutukar ganin an magance rashin adalci a ƙasar.

“Me zai sa jam’iyyar APC ta duƙufa wajen mayar da kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10 zuwa Kudu, alhali muna da hanu a Arewa.

“Arewa-maso-yamma sun baiwa APC ƙuri’u mafi yawa a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, me zai hana a ɗauki wani daga shiyyar. “Ina ganin lokaci ya yi da jam’iyyar za ta ba wa shiyyar kyautar ƙuri’u masu yawa maimakon fara neman wani daga Kudu a matsayin shugaban majalisar dattawa,” in ji shi.

Wata Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa ta amince da Mista Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa, inda ta ce shi ne ya fi dacewa da wannan muƙamin.

Leave a Reply