Ƙarin kuɗin wutar lantarki a Najeriya, ya bar baya da ƙura

0
72

Ƙarin kuɗin da Gwamnatin ta ce ta yi kan wutar lantarki ya jawo wani ruɗani wanda ya sa Hukumar Kula da samar da Wutar Lantarki ta Najeriya wato NERC ta ci kamfanin rarraba wutar lantarki ta Abuja tarar Naira miliyan 200 saboda gazawa wajen bin ƙa’idojin da ta gindaya.
Ƙarin ya nuna cewa masu sayan wuta kilowat ɗaya kan Naira 68 yanzu za su saye shi kan Naira 225, kuma wannan ƙari ne da ya shafi masu samun wutar lantarki har na tsawon sa’o’i 20 a kowace rana, kuma irin waɗannan sune aka sa su a kaso na ɗaya, waɗanda ake kira Band A a turance, sannan akwai masu kaso na biyu da ake ce masu Band B da na uku har ma da na huɗu.

Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris Malagi ya yi ƙarin haske cewa an yi ƙari ne kan waɗanda ake ganin za su iya, wanda ya zama abu na gwaji.

Idris ya ce waɗannan kuɗaɗen da ake zaton za a samu daga hanun kashi 15 cikin 100 na masu samun wuta na sa’o’i 20 a kowace rana ake so a samu kuɗin tallafi da zai sa a ba sauran ‘yan ƙasa waɗanda suka kai kashi 60 wuta su ma su mora.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Najeriya ta ƙara kuɗin lantarki

Kan batun azarɓaɓi da hukumar ba da wuta ta birnin tarayya Abuja wato AEDC ta yi na sayar da wuta kan sabon farashi kuma, Ministan Watsa labarai Mohammed Idris ya ce an ɗauki mataki na mayar wa wanda aka karɓi kuɗin sa kan kuskure da wuta da zai sha har na tsawon lokacin da kuɗin sa za su ƙare, sannan hukumar NERC ta ci tarar kamfanin AEDC tarar Naira miliyan 200.

Idris ya ce Gwamnati tana iyakacin ƙoƙarin ta saboda tana kashe Naira triliyan 2.9 duk shekara wajen samar wa ƙasa da wutar lantarki.

Amma ga Shugaban Cibiyar kare haƙƙin masu amfani da wutar lantarki a Najeriya Kola Olubiyo, ya ce yawan lalacewar hanyoyin wuta a ƙasar ya sa ‘yan ƙasa suna shan wahala, saboda haka yana ƙira ga shugaban ƙasa da ya soke sayar da hanun jarin da aka yi baki ɗaya, saboda a sake tsari da zai samar wa ƙasa da wutar lantarki na dindindin.

Shi ma Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai Kingsley Chinda ya fitar da sanarwa inda ya ce da shi da ‘yan’uwansa ba su amince da ƙarin kuɗin wutar ba kuma zai aike wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da wasiƙar neman a soke ƙarin baki ɗaya sai abubuwa sun daidaita a ƙasa.

Leave a Reply