Ƙungiyar Ƙwadago a Najeriya, ta janye batun fita zanga-zanga kan ƙarin kuɗin ƙiran waya

0
9
Ƙungiyar Ƙwadago a Najeriya, ta janye batun fita zanga-zanga kan ƙarin kuɗin ƙiran waya

Ƙungiyar Ƙwadago a Najeriya, ta janye batun fita zanga-zanga kan ƙarin kuɗin ƙiran waya

Ƙungiyar Ƙwadago a Najeriya (NLC) ta jingine batun fita zanga-zangar da take shirin yi akan ƙarin harajin ƙiran waya da sayen data da kaso 50 cikin 100.

An yanke wannan shawara ne bayan da kungiyar kwadagon ta gana da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin sakataren gwamnatin Najeriya, George Akume, a jiya Litinin.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ofishin sakataren gwamnatin, Segun Imohiosen, manufar ganawar ita ce samar da natsuwa a bangaren kwadago tare da kare muradan ‘yan najeriya.

KU KUMA KARANTA:NLC za ta gudanar da zanga-zangar gama-gari akan ƙarin kuɗin ƙira da sayen data

Ya kara da cewar ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Muhammad Idris, wanda ya zanta a madadin gwamnatin tarayya, yace manufar ganawar ita ce nazartar binciken da hukumar ncc mai kula da kamfanonin sadarwa a Najeriya tayi wanda ya kai ga karin kaso 50 cikin 100 kan harajin kiran waya da sayen data.

Bayan tattaunawa mai tsawo, bangarorin 2 sun amince da kafa wani kwamiti mai wakilai 10 da zai kunshi mutum 5 daga bangaren gwamnatin Najeriya sai mutum 5 daga bangaren NLC su sake nazarin binciken tare da mika rahoto cikin makonni 2.

Leave a Reply