Ƙungiyar matasa ta koka kan yadda ake sayar da sinadarin Kafi-Zabo a Kasuwanni

0
248
Ƙungiyar matasa ta koka kan yadda ake sayar da sinadarin Kafi-Zabo a Kasuwanni

Ƙungiyar matasa ta koka kan yadda ake sayar da sinadarin Kafi-Zabo a Kasuwanni

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ƙungiyar Matasa Don Kare Hakki da Tabbatar da Zaman Lafiya a Arewacin Najeriya, ta yi kira ga hukumar kula da ingacin abinci da magunguna ta kasa, (NAFDAC), da ta hada hannu da sauran masu ruwa da tsaki da hukumomin lafiya a matakai daban-daban, domin tabbatar da cewar ana bin dukkanin ka’idojin da suka kamata kafin siyar da sinadari mai dandanon kafi zabo wanda da ake siyarwa barkatai a cikin buhu, ko aunawa a kwano ko kuma gwangwani a kasuwanni.

A cikin jawabin bayan taro na yini uku da kungiyar ta gabatarwa matasan jihohin Arewacin Najeriya 19 don fadakar da su da sauran masu ruwa da tsaki, akan yadda ake siyar da sinadarin tace-barkatai a kasuwanni.

A cikin rubutaccen jawabin, wanda shugaban kungiyar na kasa, Injiniya Muhammad Haruna Gaza ya sanyawa hannu, ya ce kiran ya zama wajibi domin magance yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma.

KU KUMA KARANTA:Za a fuskanci zafin rana mai tsanani a Kano da wasu jihohin Arewa 17 — NiMet

Injiniya Gaza ya kara da cewar akwai muhimmiyar rawar da hukumar kula da ingacin abinci da magunguna ta kasa (KNAFDAC) da ta kula da ingancin kayayyaki ta kasa, (SON) da ta kula ta hakkin masu siye da siyàrwa ta kasa da ta nan jihar Kano, hukumomin lafiya da na da sauran masu ruwa da tsaki su hada hannu domin yakar matsalar kai da fata.

Kungiyar ta ce duk da cewar gwamnati ta bayar da izinin shigo da sinadarin Najeriya to ya na da kyau mutane su kula ba wai an halasta amfani da shi ba ne ga daidaikun mutane, a,a sai dai a masana,antu bayan an sarrafa shi.

Kungiyar ta kara da cewa yin amfani da sinadarin kafi zabo a girki na da illar gaske ga lafiya.

Leave a Reply