Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta yi ƙira ga Malaman addini su haɗa kansu

0
23
Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta yi ƙira ga Malaman addini su haɗa kansu

Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta yi ƙira ga Malaman addini su haɗa kansu

Daga Idris Umar, Zariya

Jama’atu Nasril Islam ta nemi haɗin kai da daidaito a tsakanin malaman addinin Musulunci bisa gabatowar azumin watan Ramadan.
Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta jaddada bukatar hadin kai da daidaito a tsakanin malaman addinin Musulunci gabanin zuwan watan azumin Ramadan.

KU KUMA KARANTA:Majalisar Malamai ta jihar Kano ta yanke hukunci kan rikicin masallacin Bin Uthman da ke Kundila

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana hakan a wajen taron shekara shekara da aka saba yi kafin watan Ramadan da aka gudanar a Kaduna.

Sarkin Musulmi ya ce, dole ne a hada kan Musulmi a karkashin inuwa daya duk da ana iya samun bambance bambance, amma akwai bukatar samun daidaito a tsakani, kuma wannan ya zama wajibi a wannan bangare.

Ya kara da cewa bai kamata a bar bambance bambancen da ke tsakanin da fahimta ya raba kan musulmi har ta kai ga zagin juna ba,duk yadda malami yakai ga sani tabbas akwai wanda ya fishi sani.

Sarkin Musulmi ya ce ta hanyar bin ka’idoji da dabi’a mai kyau ne kadai, malamai za su iya inganta kyakkyawar koyarwa da bayar da ilimi a watan Ramadan ga kowa da kowa

Leave a Reply