Ƙasashen Afirka sun shirya tsaf don fito da tsarin bai ɗaya na yaƙi da ta’addanci – Ministan Tsaro

0
125

Jim kaɗan bayan kammala wani babban taro na musamman a kan yaƙi da ayyukan ta’adanci a nahiyar Afrika, ƙasashen nahiyar baki ɗaya sun ce sun shirya tsaf don fitar da sabbin dabarun bai ɗaya na yaƙi da matsalolin tsaro a matakin shiyya, tare da goyon bayan wasu ƙungiyoyin ƙasashen Turai kamar EU.

An cimma wannan matsayar ne a ƙarshen taron yini biyu na yaƙi da matsaloli masu alaƙa da ta’addanci a nahiyar Afrika da aka yi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya a ƙarƙashin jagorancin ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, da goyon bayan ofishin kula da ayyukan ta’addanci na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Babban ministan tsaron Najeriya, Mallam Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa taron ya cimma matsayar fitar da dabarun bai ɗaya na nahiyar Afrika wajen yaƙi da ayyukan ta’addanci kuma ƙasashen sun shirya don ɗaukar matakai na gaba, waɗanda nan ba da jimawa ba za’a fara fitar da su.

KU KUMA KARANTA:An haramtawa Jacob Zuma tsayawa takarar shugaban ƙasa a Afrika ta Kudu

Wakiliyar mataimakin shugaban ƙungiyar tarayyar Turai mai kula da yankin Sahel Emanuela C Del Re, ta ce ganin irin ƙoƙarin da Najeriya ta yi wajen haɗa kan dukkan ƙasashen nahiyar a wani ƙoƙari na kawo ƙarshen ta’addanci a nahiyar ya sa ƙungiyar EU za ta ci gaba da ba da goyon baya a ƙoƙarin da ake yi, kuma akwai shirye-shiryen ƙungiyar da yawa da aka tsara da za su taimaka
Akasarin lokuta ana ganin rashin haɗin kan masu ruwa da tsaki shi ne matsalar da ya kamata a tunkara kai tsaye, sai dai tsohon kwamishinan yaɗa labarai kuma tsohon mamban kwamitin tsaro na jihar Adamawa, Mallam Ahmad Sajoh, ya ce an sami nasara a aikin haɗa kan dukkan masu ruwa da tsaki a fannin.

Masana dai sun ce idan ana son samun nasara a yaƙi da ta’addanci a nahiyar Afrika ya kamata masu ruwa da tsaki, da ƙungiyoyin yankunan nahiyar Afirka su taka muhimmiyar rawa wajen fitar da sabbin tsare-tsaren bai ɗaya na magance matsalar, waɗanda za su taimaka matuƙa wajen kawo ƙarshen ayyukan ‘yan ta’adda.

Leave a Reply