Gwamna Babagana Zulum a ranar Alhamis ya jagoranci rabon tallafi ciki har da abinci da sauran kayayyaki na Naira miliyan 125 ga iyalai sama da 40,000 a ƙaramar hukumar Konduga da ke Jihar Borno.
Rabon wanda aka gudanar a cibiyoyi uku, an yi shi ne domin rage raɗaɗin da mazauna yankin ke fuskanta sakamakon cire tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi a watan Mayun 2023.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa, waɗanda suka ci moriyar tallafin sun haɗa da magidanta maza 15,000, inda kowannen su ya karɓi buhun shinkafa mai nauyi kilo 25 da buhun wake kilo 10, da kuma mata 25,000 aka bai wa kowannensu kuɗi naira 5,000 da turmin atamfa guda-guda.
A cewar Gwamna Zulum, wannan wani yunƙuri ne a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ci gaba da rarraba kayan tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.
KU KUMA KARANTA: Gwamna Yobe ya ba da tallafin kuɗi a mutane 1000 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa
“Mun zo nan a Konduga. A cikin rabon na yau, kimanin mata 25,000 masu rauni kowacce ta samu turmin atamfa da Naira 5,000.
“Baya ga wannan, mun kuma raba buhun shinkafa mai nauyin kilo 25 da wake kilo 10 ga magidanta maza 15,000,” in ji Zulum.
Ana iya tuna cewa, a watan Yulin da ya gabata ne Gwamnatin Borno ta raba kayayyakin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ga magidanta kimanin 300,000 a faɗin jihar, inda aka bai wa al’ummomin da rikicin ta’addanci ya fi shafaZulum ya raba wa iyalai 40,000 tallafin abinci da kuɗi a Konduga
Gwamna Babagana Zulum a ranar Alhamis ya jagoranci rabon tallafi ciki har da abinci da sauran kayayyaki na Naira miliyan 125 ga iyalai sama da 40,000 a Karamar Hukumar Konduga da ke Jihar Borno.
Rabon wanda aka gudanar a cibiyoyi uku, an yi shi ne domin rage radadin da mazauna yankin ke fuskanta sakamakon cire tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi a watan Mayun 2023.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa, wadanda suka ci moriyar tallafin sun hada da magidanta maza 15,000, inda kowannen su ya karbi buhun shinkafa mai nauyi kilo 25 da buhun wake kilo 10, da kuma mata 25,000 aka bai wa kowannensu kudi naira 5,000 da turmin atamfa guda-guda.
A cewar Gwamna Zulum, wannan wani yunkuri ne a kokarin da gwamnati ke yi na ci gaba da rarraba kayan tallafi ga masu karamin karfi a jihar.
“Mun zo nan a Konduga. A cikin rabon na yau, kimanin mata 25,000 masu rauni kowacce ta sami turmin atamfa da N5,000.
“Baya ga wannan, mun kuma raba buhun shinkafa mai nauyin kilo 25 da wake kilo 10 ga magidanta maza 15,000,” in ji Zulum.
Ana iya tuna cewa, a watan Yulin da ya gabata ne Gwamnatin Borno ta raba kayayyakin rage radadin cire tallafin man fetur ga magidanta kimanin 300,000 a fadin jihar, inda aka bai wa al’ummomin da rikicin ta’addanci ya fi shafa muhimmanci.