Zulum ya ƙaddamar da rukunin gidaje 100 na na gwamnatin tarayya a Gwoza

3
263

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Laraba ya ƙaddamar da wasu gidaje 100 da gwamnatin tarayya ta gina a ƙaramar hukumar Gwoza.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ce ta gina aikin a ƙarƙashin shirinta na ci gaba mai ɗorewa, SDGs.

Gwamna Zulum, wanda mataimakinsa, Usman Kadafur ya wakilta a wajen bikin ya yaba wa manufar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na ganin ‘yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi sun samu gidaje masu inganci da rahusa.

Ya yi nuni da cewa, ayyukan samar da gidaje za su magance matsalolin ƙarancin gidaje da kuma inganta ayyukan sake tsugunar da al’ummar jihar da tashe-tashen hankula suka yi wa ɓarna.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Zulum ya sake buɗe kasuwar shanu ta Gamboru

A nata jawabin, babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin SDG, Adejoke Adefulire, ta ce an tsara aikin ne domin tallafawa tsarin ci gaban jihar Borno na BoSDF na tsawon shekaru 25.

Hakan a cewar ta, an yi shi ne da nufin aza harsashi mai inganci da samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar. Misis Adefuilire ta ce gidajen an yi su ne domin mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

“A shekarar 2030, kashi 70 cikin 100 na al’ummar Borno za su tsunduma cikin harkokin rayuwa, tun daga makaranta da kuma aiki kuma wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin tallafawa irin waɗannan shirye-shiryen”, in ji Misis Adefulire.

3 COMMENTS

Leave a Reply