Zulum ya ƙaddamar da gidaje 200 a Nganzai LG

0
374

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya ƙaddamar da gidaje 200, wanda gwamnatin tarayya ta gina a Gajiram a ƙaramar hukumar Nganzai ta jihar.

Da yake ƙaddamar da aikin, Gwamna Zulum ya ce, ofishin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa, a ƙarƙashinsa na ci gaba mai ɗorewa, SDGs, ayyuka.

Ya ce aikin na da nufin samar da matsuguni ga mutanen da rikicin ta da ƙayar baya ya raba da muhallansu a jihar. Ya bayyana cewa samar da gidajen zama wani muhimmin al’amari ne na sake tsugunar da al’umma da kuma gyara ga al’ummomin da rikicin ya shafa.

“Hakan zai inganta yanayin rayuwar jama’a, da kuma samar da kwanciyar hankali,” in ji shi. Gwamnan ya yabawa shugaba Buhari da ofishin SDG bisa samar da gidajen jama’ar Gajiram.

KU KUMA KARANTA: Zulum ya ƙaddamar da rukunin gidaje 100 na na gwamnatin tarayya a Gwoza

Ya kuma nanata ƙudurinsa na sake tsugunar da al’umma da kuma gyara waɗanda rikicin ya shafa.

A nata jawabin babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin SDG, Adejoke Adefulire, ta yabawa Gwamna Zulum da dukkan masu ruwa da tsaki da suka ba da gudumawa wajen samun nasarar aikin domin amfanin al’umma.

Ta ce shugaban ya yi matuƙar kishin ƙasa wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar, da gina al’ummomin da ‘yan ta da ƙayar baya suka lalata.

Leave a Reply