Zaɓen 2023: A daina yaɗa sakamakon zaɓe na ƙarya, in ji ‘yan sanda

2
438

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta lura da yaɗa sakamakon zaɓen da ake yi a kafafen sada zumunta da sauran kafafen yaɗa labarai, wanda hakan ya saɓawa manufofi da ƙa’idojin hukumar zabe mai zaman kanta.

Kakakin rundunar’yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar lahadi inda ya ce, “’Yan sanda sun fahimci wannan al’amari a matsayin wani yunƙuri na yunƙuri na zafafa harkokin siyasa da kuma haifar da hargitsi bayan zaɓuka.

KU KUMA KARANTA: Atiku ya lashe zaɓe a mazaɓar elRufa’i da ta Ahmed Lawan

Muna ɗaukar wannan a matsayin rashin aiki, rashin kishin ƙasa, da kuma ɓarna. “Hukumar ‘yan sanda a nan tana gargaɗi masu yaɗa sakamakon zabe na bogi da su ƙaurace wa irin waɗannan munanan ayyuka su jira sakamakon hukumar INEC, wanda yake ingantacce kuma mai inganci.

“Hukumar ‘yan sanda ta bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulansu, kuma su bi doka da oda, yayin da waɗanda aka ba wa takardar izinin kaɗa ƙuri’a a yau an bukaci su kasance cikin tsari da bin doka da oda domin mun sake tabbatar da dabarunmu na tsaro domin ganin an kammala zaɓen cikin sauki babban zaɓen 2023.” In ji sanarwar

2 COMMENTS

Leave a Reply