Zanga-Zanga: Kotun Tarayya ta aika mutum 10 gidan yari

0
33
Zanga-Zanga: Kotun Tarayya ta aika mutum 10 gidan yari

Zanga-Zanga: Kotun Tarayya ta aika mutum 10 gidan yari

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta aika da mutum 10 waɗanda ake zargi da hannu a zanga-zangar #EndBadGovernance zuwa gidan yari.

Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya ya aika da maza tara gidan gyaran hali na Kuje sannan ya aika da mace ɗaya zuwa gidan yarin Suleja.

Haka kuma alƙalin ya saka ranar 11 ga watan Satumba a matsayin ranar da zai yanke hukunci dangane da buƙatar bayar da belin da waɗanda ake zargin suka shigar a gaban kotun, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

KU KUMA KARANTA: An kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Chicago

Aika su gidan yarin na zuwa ne bayan an gabatar da su a gaban kotu inda ake tuhumar su da cin amanar ƙasa da yi wa gwamnati bore da kuma yunƙurin hargitsa Najeriya.

Mutum goman da aka gurfanar a gaban kotun sun haɗa da Michael Adaramoye da Adeyemi Abayomi da Suleiman Yakubu da Opaoluwa Simon da Angel Innocent.

Sauran sun haɗa da Buhari Lawal da Mosiu Sadiq da Bashir Bello da Nuradeen Khamis da kuma Abdulsalam Zubairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here