Zanga-Zanga: An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

0
86
Zanga-Zanga: An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

Zanga-Zanga: An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya sanya dokar hana fita tsawon awa 24 kuma ta fara aiki nan take.

Majalisar tsaron jihar ta amince da kafa wannan doka ne bayan zaman da ta yi a ranar Litinin.

Sanarwar da Kwamsihinan Tsaro na jihar, Samwel Aruwan ya fitar ta ce kwararan hujjoji sun riga sun bayyana cewa bata-gari sun shiga rigar zanga-zangar tsadar rayuwa suna fasa shaguna da saceewa da kuma lalata kayan jama’a da na gwamnati a jihar.

Aruwan ya buƙaci al’ummar wuraren da dokar ta shafa da su kasance a gidajensu tare da ba wa jami’an tsaro haɗin kai domin tabbtar da wannan doka.

KU KUMA KARANTA: Amnesty ta buƙaci gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike kan kashe masu zanga-zanga a jihar

A cewarsa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da lura da halin da ake ciki a jihar da nufin daukar mataki na gaba.

Wannan doka na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da masu zanga-zangar tsadar rayuwa suka yi arangama da jami’an tsaro a garin Kaduna.

Masu zanga-zangar, waɗanda akasarinsu matasa ne da ƙananan yara, sun fito kan tituna ne ɗauke da tutar ƙasar Rasha.

Masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati sun riƙa rera wakokin haɗin kai a unguwannin da ke garin Kaduna, irin su Kawo da Unguwar Shanu da sauransu.

Sun kuma yi sa-in-sa da sojoji da ’yan sanda da suka yi ƙoƙarin shawo kansu a yayin tattakin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here