Zan yi duk mai yiwuwa don ganin an samar da jihar Karaduwa daga Katsina – Sanata Barau Maliya
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Mataimakin shugaban majalisar dattawa daya fito daga Jihar Kano, Barau Jibrin, ya bayyana goyon bayansa ga samar da jihar Karaduwa daga jihar Katsina.
Barau Maliya, wanda ke shugabantar kwamitin majalisar dattawa kan duba kundin tsarin mulkin kasa, ya bayyana irin karfin noma da shiyyar ke da shi, ya kuma tabbatar da cewa ta cancanci ƙara samun jiha.
Ya yi wannan jawabi ne a garin Funtua da ke Jihar Katsina, a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan da kuma wayar da kan jama’a da Sanata Muntari Dandutse, mai wakiltar mazabar Katsina ta Kudu ya shirya.
A cewarsa, kirkirar jihar Karaduwa, daga Katsina batu ne mai kyau, kyakkyawan fata ne daga mutanen Karaduwa.
“Wannan yanki ne na noma, suna da duk abin da ake buƙata don samun jiha.
Amma kun san ka’idojin tsarin mulki don samun jiha, Ina martaba ra’ayoyinsu, ina goyon bayansu,” a cewar mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Maliya, ya bada tabbacin cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin al’umma su cimma burinsu na samar da Jihar Karaduwa.
“Zan yi duk mai yiwuwa. Kar ku manta, mu makwabta ne. Shiyyar da nake wakilta a majalisar dattawa tana da iyaka da wannan yanki, don haka na san abin da suke bukata,” a cewar Maliya.
KU KUMA KARANTA:‘Yansanda a Kano sun fitar da sabbin matakan tsaro a watan Azumi
Dandutse, a yayin taron, ya zayyana kayayyakin da aka tanada domin karfafawa, wadanda suka hada da shinkafa tirela takwas.
Ya kuma raba buhunan taki guda 5,439, buhunan masara 3,795, kekunan dinki 384, da injinan nika 110 domin tallafa wa mazabun a cikin watan Ramadan.
Shima da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar, Bala Abu-Musawa, ya bi sahun ‘yan majalisar dokokin kasar na ra’ayin kirkiro jihar Karaduwa.
Ya yabawa Dandutse bisa goyon bayan da ya bayar wajen bayar da shawarwarin kafa Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Tarayya a Karamar Hukumar Funtua.