Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
Gwamnan Jihar Ribas Mista Nyeson Wike ya bayyana cewa babban kudirinsa in zama shugaban tarayyar Najeriya shi ne ya magance matsalar tsaron da ke addabar kasar a matakin farko.
Nyeson Wike ya bayyana hakan ne a garin Kaduna lokacin da ya kai ziyara ganawa da wakilan Jam’iyyar PDP masu zaben wanda zai tsaya takarar shugaban kasa su 74 daga Jihar.
A wajen babban taron da aka yi domin tarbar bakuncinsa tare da tawagarsa a dakin taro na Sakatariyar Jam’iyyar da ke NDA Kaduna, Wike ya bayyana cewa zai fara ne da yin maganin matsalar tsaro idan yan Najeriya suka zabe shi ya zama shugaban kasa.
Nyeson Wike ya kuma shaida wa masu zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar cewa idan sun zabe shi a zaben fidda gwani a matsayin dan takarar kujerar shugabancin Najeriya karkashin PDP, to kowa ya tabbatar cewa za a samu nasarar lashe zabe ba tare da wata tantama ba ko kadan.
“Ina kira ga masu zaben dan takarar kujerar shugaban kasa daga PDP da su tabbatar sun zabi wanda zai iya lashe zaben kasa baki daya domin a samu sauki a kasa baki daya”.
Kamar yadda jama’a suka sani a can shekarun baya babu wani shugaba a yankin Arewacin Najeriya da bashi da gida a Kaduna, domin wuri ne na zaman lafiya da lumana kuma jama’a da dama komai dare su na tafiya zuwa Kaduna daga Abuja, kai ko ni kaina ina minista ina zuwa Kaduna ne ta hanyar yin amfani da mota domin ko’ina lafiya kalau amma yanzu fa? kowa ya san rashin tsaro ya yi yawa.
Nyeson Wike ya kuma yi kira ga wakilan Jam’iyyar da ke Jihar Kaduna da su bashi kuri’a Sittin (60) daga cikin kuri’u 74 na masu zaben wanda zai tsayawa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a shekarar 2023 mai zuwa, koda yake za a yi zaben fitar da Gwanin ne a ranar 28 da 29 na watan Mayu mai zuwa don haka su zabe shi saboda shi ne dan takarar da zai iya tsayawa har sai nasara ta samu a koda yaushe.
Wike ya kuma shawarci duk yayan PDP da su hada kansu domin ya yi alkawarin zai taimaka masu idan zabe ya zo, saboda Ya’yan PDP a Jihar Kaduna sun yi rawar gani a zaben kananan hukumomin da aka yi a Jihar domin sun samu kananan hukumomi shida (6) daga cikin kujerun da Jihar ke da su 23 don haka a hada kai domin hakan shi ne mafita”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya bayyana irin jajircewar Nyeson Wike da cewa ta haifarwa da jam’iyyar PDP da kuma wadanda suka yi hakuri a cikin ta da nasarar da ake ciki a halin yanzu .
Sanata Makarfi ya kuma bayyanawa taron taimakon kudin da Nyeson Wike ya bayar domin tallafa wa yan gudun hijira da suke a Kaduna na kudi har naira miliyan dari biyu lakadan.
Makarfi ya kuma yi alkawarin yin amfani da kudin kamar yadda ya dace ga wadanda aka bayar da kudin dominsu.
Acewarsa, duk wanda ya damu da kai hakika kaima ka damu da shi.
Hajiya Hauwa Kida, ta gabatar da jawabi a madadin mata cikin harshen Turanci inda ta bayyana Nagarta da irin ayyukan alkairin da Gwamna Wike kuma dan takarar PDP yake yi wadandada ta bayyana su a matsayin abin farin ciki.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna Nuhu Bajoga ya bayyana halayen Gwamna Wike da cewa sai wanda ya matsa kusa da shi kawai zai tabbatar da nagartarsa, saboda haka ya ce Nyeson Wike ya cancanci samun kuri’u 60 daga Jihar Kaduna.
Tun da farko sai da jagoran tafiyar fafutukar neman zaben Nyeson Wike a matsayin mai neman a tsayar da shi dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, wato tsohon Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Hassan Dan kwambo, ya bayyana dalilan da suka sanya dan takarar nasa ya cancanci a zabe shi ya tsayawa PDP takarar shugaban kasa.
Ya’yan jam’iyyar musamman masu kuri’ar zaben dan takara a ranar zabe sun bayyana gamsuwa da jindadinsu da irin yadda Gwamna Nyeson Wike ke taimakawa Jam’iyyar.
Wasu daga cikin jiga Jigan yayyan Jam’iyyar PDP da suke cikin tawagar Nyeson Wike sun hada da Sanata Yakubu Lado Dan Marke, Sanata Nazifi, honarabul Yakubu Barde ( no shaking) a matsayin kodinetan tafiyar Nyeson Wike a Jihar Kaduna da dai sauran kusoshin PDP da dama.
[…] KU KUMA KARANTA: Zan Magance Matsalar Tsaro A Najeriya – Gwamna Wike […]