Daga Shafaatu Dauda, Kano
Mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya DIG Hafiz Muhammad Inuwa da ke kula da harkokin zaɓen shekarar 2023 ayankin jahohin arewa maso yammacin Nijeriya , ya gargadi ‘yan siyasa da magoya bayan su, dasu kaucewa yin wani abu da zai tada hankulan masu zaɓe.
DIG Hafiz M. Inuwa ya bayyana cewa babban sufeton ‘yan sanda na ƙasa IGP Usman Alkali Baba ya umarce su, da su gargaɗi ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki da su jawa magoya bayan su kunne gabanin zaɓen da ke tafe a ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023.
DIG Hafiz M. Inuwa ya bayyana hakanne a jahar Kano ,a ci gaba da shirye-shiryen da rundunar ‘yan sanda ta ƙasa ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu .
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda dubu 18,748 aka jibge a Kano saboda zaɓen Gwamna
Ya ƙara da cewa fatan su, shi ne a yi zaɓe lafiya a kammala lafiya, ba tare da nuna siyasa da gaba ba.
‘’duk wani ɗan siyasa indai yana son ci gaban Kano , to zaman lafiya shi ne ci gaban, so ake a zauna lafiya.
‘’kuma na zo da jawabi, in gargaɗe su, Wallahi ba zamu yi ƙasa a gwiwa ba wajen maganin duk wani da ya nemi ya tada fitina, saboda haka ina tabbatar muku da cewa duk wanda ya nemi ya ɗau makami ko dan ya hana wani fito wa zaɓe kodan ya jikkata wani to ‘wallahi tallahi fushin hukuma ne a tattare dashi”. In ji DIG Hafiz.
Ya ce ba zasu raga wa kowa ba duk girmansa kowaye , domin ci gaban Najeriya da ci gaban Kano da kuma zaman lafiya shi ne agaba.
‘’In kunne yaji jiki ya tsira , wanda kuma ya ke ganin zai yi wani abu akasin haka to ga fili ga mai doki’l”
Tun kafin wannan lokacin ne kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa sun tanadi dakarun ‘yan sanda masu yawa dan tabbatar da tsaro a zaɓen ranar 18 ga watan Maris 2023.
[…] KU KUMA KARANTA: Zamu yi maganin duk wanda ya fito da makami komai girmansa- DIG ga ‘yan siyasa […]