Zaben Atiku Abubakar Zai Samar Da Jagoranci Nagari A Najeriya – Inji Chaye

0
483

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AN bukaci ‘yan Najeriya da su zabi tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Wazirin Adamawa Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa a zaben Shekara ta 2023 domin samun shugabanci mai nagarta kuma bisa kwarewa.

Wani jigo a tafiyar siyasar gidan Wazirin na Adamawa Alhaji Musa Yola, wanda aka fi sani da Musa Chaye shi ne ya bayyana hakan a hirar su da wakilin mu, inda ya nunar da cewa Atiku Abubakar mutum ne mai matukar tausayi da kaunar mutanen Najeriya wanda idan ya zamo shugaban kasa za a sami sauyi mai gamsarwa ta kowane fanni.

Ya ce “Atiku Abubakar ya dade yana bada gudummawar sa ga ci gaban kasar nan tare da rike mukamai masu tarin yawa wadanda kuma sun isa a gamsu cewa Najeriya za ta sami jagora kuma mai kyawawan manufofi ga mutanen Najeriya.

Alhaji Musa Yola, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana cikin wani yanayi na bukatar samun shugaban ci nagari duba da yadda wannan gwamnati ta Jam’iyyar APC ta gaza cika alkawuran da tayi wa mutanen Najeriya a lokutan yakin neman zabe wanda hakan ya nuna a fili cewa Jam’iyyar PDP ita ce take da tsarin bunkasa kasar nan.

Haka kuma ya sanar da cewa da yardar Allah gwamnatin Atiku Abubakar Wazirin Adamawa zata farfado da tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma cikin nasara musamman ganin cewa yana da kwarewa a sha’anin mulki da kuma iya tafiyar da shugabanci a tsari irin na dimokuradiyya.

Daga karshe, Musa Chaye ya sanar da cewa sun kammala shiri tsaf domin ci gaba da bayyana irin kyawawan manufofin da Atiku Abubakar yake dasu domin ganin kasar nan ta sami ci gaban da ake bukata ta yadda al’ummar kasa zasu amfani arzikin da Allah ya shimfida a kasar a matsayin sa na masanin tattalin arziki da harkokin kasuwanci.

Leave a Reply