Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
SHUGABAN kwamitin yada labarai da fadakarwa na kwamitin shirya zaben shugabannin Jam’iyyar APC na kasa Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Abdullahi Sule, ya tabbatar wa manema labarai cewa ana shirin fito da jadawalin sunayen hadin kai dangane da zaben shugabannin APC na kasa da ake kokarin yi a yanzu.
Abdullahi Sule ya ci gaba da cewa kamar yadda kowa ya sani tsarin mulkin Najeriya ya bayar da damar ayi maslaha ko zabe don haka Jam’iyyar APC ke kokari game da babban taron APC na kasa ake fatan samun maslaha daga kowace shiyya ta kasa.
“Don haka ana fatan samun jadawalin sunayen hadin kai na yayan Jam’iyyar da zai tabbatar da an samu sahihin hadin kai a tsakanin Ya’yan APC”.
Abdullahi Sule ya shaidawa manema labarai cewa tun da Jam’iyyar ta samu nasarar kafa Gwamnati an samu ci gaba sosai a fadin kasa baki daya a bangarori daban daban.
Daga cikin nasarar da aka samu akwai farfadowa daga matsalar tattalin arziki sakamakon annobar Korona, da kuma samun inganta tattalin arzikin kasa, nasarar kaucewa biyan kudin haya a ofishin Jam’iyyar APC na kasa, wanda sakamakon hakan a yanzu aka rada wa ofishin Jam’iyyar sunan Buhari tun da an sayi ofishin ya zama na Jam’iyyar baki daya.
“An kuma samu nasarar bude kamfanin Taki na Dangote da zai samar da tan miliyan uku a shekara ga kuma babbar katafariyar matatar man fetur ita ma katafariya ta Dangote duk nasara ce da Gwamnatin APC ta samu.
Ga kuma dimbin nasarorin bunkasa harkokin Noma da suka hada da Noman Shinkafa, Masara da sauran dukkan fannonin Noma baki daya.
Sule ya kara tabbatar da cewa babu wani hadi a game da irin nasarorin da APC ta samu a tun daga lokacin da aka kafa zuwa yanzu, ba za a hada ta da abin da wasu suka yi na tsawon lokaci mai tsawo a baya ba.
An kuma samu kafa jam’iyyar APC ne sakamakon hada kar da aka samu tsakanin jam’iyyun CPC, ANPP, ANC da wani bangare na APGA duk a wancan lokacin, amma a duba sosai irin yadda aka cimma gagarumar nasara da dimbin ci gaban da aka samu.
“Don haka muka kira ga daukacin yayanta da suka yi rajista su miliyan sama da Arba’in da ma wadanda ke yi a halin yanzu domin zama yan jam’iyya duk su taru a ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga APC domin a kara cin moriyar Dimokuradiyya”.
Kuma idan an samu yin Maslaha tsakanin masu neman wadansu kujerun zama shugabannin jam’iyya a kowane irin mataki, za a mayarwa da kowa kudin da ya sayi fom na tsayawa takara.