Za mu ɗauki kowane mataki wajen ɗakile hauhawar farashin kayayyaki – Cardoso

0
22
Za mu ɗauki kowane mataki wajen ɗakile hauhawar farashin kayayyaki - Cardoso

Za mu ɗauki kowane mataki wajen ɗakile hauhawar farashin kayayyaki – Cardoso

Babban Bankin Najeriya (CBN) zai ɗauki kowane irin mataki da kuma ”kayan aikin da suka dace” wajen daƙile hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, a cewar shugaban bankin Olayemi Cardoso a ranar Talata.

A karon farko cikin watanni uku hauhawar farashin kayayyaki ta shekara-shekara a ƙasar da ke da mafi yawan al’umma a Afirka ya ƙaru a watan Satumba, inda ya kai kashi 32.70 cikin ɗari, sakamakon hauhawar farashin abinci da makamashi.

Hauhawar farashin ta ta’azzara ne sakamakon matakin da gwamnati ta ɗauka na cire tallafin man fetur da wutar lantarki da kuma rage darajar kuɗin ƙasar Naira har sau biyu bayan hawan shugaba Bola Tinubu kan mulki a bara.

Cardoso ya shaida wa taron FT Africa a birnin Landan cewa, yayin da ake sa ran samun sauƙi a watanni masu zuwa, hauhawar farashin abinci ”ta daɗa yin ƙamari”. Sai dai ya jadadda cewa bankin na aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnati domin shawo kan lamarin.

Bai kamata Najeriya ta yi ƙasa a gwiwa ba a yunƙurinta na sake fasalin ƙasa, la’akari da yadda take janyo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje, in ji Cardoso, yana mai nuni da ziyarar da shugaban Citigroup Jane Fraser da Jamie Dimon na JPMorgan suka kai ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Hauhawar farashin kayaki ta sake ta’azzara bayan lafawar watanni 2 – NBS

“Ana ci gaba da nuna sha’awa a ƙasar sosai, duba da cewa darajar kudin Najeriya tana ƙara daidaita, lamarin da ke ƙara tasiri sosai a tattalin arzikinmu.”

Cardoso ya ce matakan da CBN ya ɓullo da su suna ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa, sannan a halin yanzu babu wasu ƙorafe-ƙorafe da ake samu game da rashin kuɗaɗen waje idan aka kwatanta da lokutan baya da mutane ƙalilan ne kawai suke iya samu.

“A yanzu haka, kasuwa tana ƙara haɓaka kuma ana samun kuɗaɗen waje (forex),” in ji shi.

Adadin kuɗaɗen ajiya na ƙasashen waje a yanzu ya haura dala biliyan 40, kana Cardoso ya ce Babban Bankin Najeriya zai riƙ yin ƙarin haske game da asusun ajiyar kuɗaɗen a-kai-a-kai daga farkon shekarar 2025.

Leave a Reply