Daga Ibraheem El-Tafseer
Shugaban Najeriya ya bayyana cewa yana bibiyar halin da ake ciki a Gabon “cikin damuwa” sakamakon juyin mulkin da sojoji suka sanar a ranar Laraba.
Tinubu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Ecowas, ta raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma, ya ce yana duba hanyoyin da zai mayar da martani tare da sauran shugabannin Afirka.
Da yake ba da misali da juyin mulkin baya-bayan nan, Tinubu ya ce “annoba” ta kama Afirka, kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya bayyana.
KU KUMA KARANTA: Sojoji sun sanar da Janar Nguema a matsayin shugaban ƙasar Gabon
A ranar Laraba ne sojoji a Gabon suka sanar da ƙwace mulki kuma suka yi wa Shugaba Ali Bongo mai shekara 64 ɗaurin talala.