Za mu ci gaba da zanga-zanga saboda jawabin Tinubu bai taɓo buƙatunmu ba – Ƙungiyar ‘The Take it Back Movement’
Daga Ibraheem El-Tafseer
Ƙungiyar ‘The Take it Back Movement’, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka shirya zanga-zagar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya ta ce ”zanga-zangar za ta ci gaba”, duk kuwa da ƙiran dakatar da ita da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi.
Cikin jawabin da ya gabatar wa ƙasar ranar Lahadi da safe, shugaba Tinubu ya yi ƙira ga waɗanda suka shirya zanga-zangar su dakatar da ita tare da rungumar hanyar tattaunawa.
To sai cikin wani saƙo da ƙungiyar ‘The Take it Back Movement’ ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce shugaban bai taɓo buƙatunsu cikin jawabin nasa ba, sannna ya ka sa ɗaukar alhakin ”kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zangar”.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International ta ce mutum 13 jamai’an tsaro suka kashe ranar Alhamis.
To sai rundunar ‘yansandan ƙasar ta musanta amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima kan masu zanga-zangar, tana mai cewa mutum bakwai ne kawai suka mutu.
KU KUMA KARANTA: Aƙalla masu zanga-zanga 700 aka kama a Najeriya
Rundunar ‘yansandan ta kama kusan mutane 700.
A ranar Lahadi wasu mutane da ake zargin ɓata-gari ne sun tarwatsa masu zanga-zangar a birnin Legas da ke kudancin ƙasar.
Masu zanga-zangar na buƙatar gwamnati ta mayar da tallafin man fetur da ta cire domin rage farashin fetur da na lantarki, haka kuma suna buƙatar hukumomin ƙasar su magance matsalar tsaro da cin hanci da rashawa.
Ana sa ran ci gaba da zanga-zangar a faɗin ƙasar har zuwa ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban ƙasar dai ya umarci jami’an tsaro su ci gaba da tabbatar da doka da oda.
Yayin da ake fargabar samun ƙarin arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.