Za mu bai wa Google goyon baya don samar da ayyukan yi miliyan ɗaya ga ‘yan Najeriya – Tinubu

2
308

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce a shirye gwamnatinsa take wajen mara wa babban kamfanin fasaha na Google baya don samar da ayyukan yi miliyan guda a ƙasar.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da mataimakin shugaban kamfanin Mista Richard Gingras ya ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake ya fitar, Shugaban na Najeriya ya ce Najeriya na da matasa masu basira da fasaha, waɗanda koyaushe a shirye suke wajen koyon sabbin abubuwa musamman a wannan zamani na bunƙasar fasahar zamani.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya gana da sakataran gwamnatin tarayya don samar da ayyukan ci gaba a jihar

Yana mai cewa kamfanin google na da dukkan abubuwan da matasan Najeriya ke buƙata don bunƙasa fasaharsu.

“Ina farin ciki cewa Google a shirye yake ya yi aiki da mu. kun amsa kiranmu wajen samar wa matasanmu sabbin ayyukan fasahar zamani. Kuna mara wa yunƙurinmu baya na bunƙasa sabbin hanyoyin tattalin arziki na zamani. A shirye muke mu yi aiki da ku kan yunƙurinku na amar da ayyukan yi miliyan guda ga matasanmu”, in ji shugaban na Najeriya.

Ya ƙara da cewa “Za mu ba ku duk goyon bayan da kuke buƙata domin cika wannan buri naku”.

Najeriya na da miliyoyin matasa marasa aikin yi a ƙasar wadda ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afirka.

2 COMMENTS

Leave a Reply