Za a yi kwanaki uku ana ruwa marka-marka a jihohin Arewa
Hulu mar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin Arewa sakamakon mamakon ruwan marka-marka da za a samu.
Hulu mar ta ce jihohin da suka haɗa da Kano da Katsina da Zamfara da Jigawa da Kebbi da Kaduna da Adamawa na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa, don haka ta yi ƙira ga mahukunta a jihohin su ɗauki matakan kare al’ummominsu.
Tuni ambaliyar ta fara yin ɓarna a wasu jihohin, inda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi.
Alhaji Bashir Idris Garga, Darakta a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ya ce ruwan saman da za a yi na kwana uku ba ƙakƙautawa zai sa magudanun ruwa da dama da ba a cika damuwa da yashe su ba, su cike wanda hakan ka iya sa ruwan ya malala har ya je ya yi ɓarna.
KU KUMA KATANTA:Ruwan sama a Bauchi ya yi sanadiyar mutuwar mutum 5
Saboda haka ya kamata a ɗauki mataki ƙwarai da gaske ya zama cewa ambaliyar ba ta yi ɓarna fiye da yadda ake zato ba,’’ in ji Garba.
Daraktan ya ce, akwai wasu matakai da ake ɗauka na gaggawa irin su samun buhunhuna a cika da yashi a yi katanga don a canza wa ruwan hanya yadda ba zai shiga ya yi ɓarna ba.
Darakatan ya ƙara da cewa, bayan haka, ya kamata a yashe magudanun ruwa kuma a dage a sanar da ’yan uwa da abokan arziki kan sanarwar da aka bayar kuma ya kamata a ɗauki matakan riga-kafin lamarin.