Za a rufe titi na tsawon mako 6 saboda Kwaɗi za su tsallaka
Daga Ibraheem El-Tafseer
Wata ƙaramar hukuma a kudu maso yammacin Ingila ta ɗauki wani mataki da ba a saba gani ba na rufe wani titi tsawon makonni shida domin bai wa kwaɗi da dangoginsu damar tsallakawa zuwa tafkinsu na asali domin haihuwa.
A duk shekara, motoci na kashe ɗaruruwan dabbobi kamar su kwaɗi da danginsa a kan titin da ke kusa da birnin Bath.
KU KUMA KARANTA:Mace ta farko da ta musulunta a Liverpool, Ingila
Bayan ɗaukar wannan mataki, a yanzu dabbobin za su iya tsallakawa cikin aminci a tsaka da lokacin da suka fi hayayyafa.
Adadin kwaɗin da ake da su a Birtaniya ya ragu da kashi biyu cikin uku a shekaru 30 da suka gabata saboda lalata musu muhallansu da akeyi da kuma sauyin yanayi.









