Za a bai wa ‘yan Najeriya rancen kuɗi don su mallaki jiragen ruwa

0
400

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da gagauta bada rancen kuɗi ga ‘yan ƙasa masu ra’ayin mallakar jiragen ruwa.

Shugaba Buhari ya bada umarnin ne a ƙudirinsa na ganin ‘yan Nijeriya sun mallaki jiragen ruwa cikin sauƙi,

Ministan harkokin sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai inda ya ce an amincewa bankunan Union da Zenith da Polaris da UBA da kuma Ja’iz a matsayin cibiyoyin da za su rarraba kuɗaɗen.

Ministan yayi nuni da cewa ma’aikatar shi ta fara tuntubar ministar kuɗi, da gwamnan babban bankin Najeriya don fara aiwatar da tsarin.

KU KUMA KARANTA:Sojojin Sama Ne Za Su Dinga Raka Jirgin Ƙasa Na Kaduna-Abuja – Amaechi

Ya kuma bayyana fatan cewa wannan tsarin zai kara bunkasa hada-hadar sufurin jiragen ruwa a ɓangaren iyakokin ruwan ƙasar nan.

A nashi tsokacin, Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwa na Najeriya, Dakta Bashir Yusuf Jamoh ya bayyana cewa, kuɗaɗen da aka amince a bada rance sun haura sama da naira miliyan dubu goma sha shida, kimanin dala miliyan ɗari uku da hamsin.

Shi dai wannan tsarin an fara shi ne a shekarar 2003 don ƙarfafa gwiwar ‘yan Najeriya su mallaki jiragen ruwa don gudanar da kasuwanci inda za su biya kashi goma sha biyar, ita kuma hukumar NIMASA ta bada kashi talatin da biyar, sai kuma bankuna su bada kashi hamsin na kuɗin.

Leave a Reply