Zaɓen gwamna a Kano: Ɗantata ya musanta goyon bayan APC

Attajirin ɗan kasuwa kuma dattijon jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata, ya musanta rahotannin da ke cewa yana goyon bayan Nasiru Gawuna, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kano.

Rahotanni da dama a fagen siyasar Kano sun yi ta yawo inda aka yi nuni da cewa attajirin ya goyi bayan Gawuna, kuma da yawa daga cikin waɗanda ke yawo da rahotannin sun danganta amincewa da zargin da ake yi na tataɓurza tsakanin dattijon da kuma Rabiu Musa Kwankwaso, shugaban jam’iyyar NNPP, babbar jam’iyyar adawa a jihar Kano.

Sai dai Ɗantata, ta hanyar wani sakon da babban sakataren sa Mustapha Junaid ya wallafa a Facebook, ya bayyana cewa shi baya ɓangaranci.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda dubu 18,748 aka jibge a Kano saboda zaɓen Gwamna

Junaid ya bayyana cewa Dantata bai taɓa amincewa da wata jam’iyya ko ɗan takara ba.

“Ina sanar da kowa cewa Aminu Ɗantata bai umurci kowa ya zaɓi Gawuna ba, kuma bai amince da wani ba, domin shi uba ne ga kowa,kuma haka ya kamata masu yaɗa wannan labarin na ƙarya su daina kai tsaye, kuma cikin gaggawa, su goge duk wani rubutu da aka yi dangane da hakan,” in ji sakon.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *