Zaɓen 2027: Tsakanin Kwankwaso da Shekarau waye ke zawarcin wani?
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana shirin sake haɗa kai da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, a ƙoƙarin shirye-shiryen zaɓen 2027 mai zuwa.
Haka kuma, Shekarau ya bayyana cewa babu wata gaba tsakaninsa da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, duk da saɓanin siyasar da ya raba su a baya.
Tsohon Ministan Ilimi, wanda ya koma jam’iyyar PDP kafin zaɓen 2023, ya kafa wata sabuwar kungiya mai suna League of Northern Democrats (LND) domin ƙoƙarin kafa wata sabuwar fuskar siyasa.
Ba’a tabbatar ba ko wannan matakin da Shekarau ke dauka na kokarin kusantar Kwankwaso yana daga cikin dabarun siyasa na sabuwar kungiyar LND, duba da yadda Shekarau da tawagarsa suka kara kaimi wajen tuntubar manyan ‘yan siyasa a fadin kasa kwanan nan ba.
KU KUMA KARANTA:Indai sahihin zaɓe za a yi NNPP za ta kayar da APC da PDP – Kwankwaso
Shekarau ya bayyana cewa sabanin da suka samu da Kwankwaso ba wai na kashin kai bane, illa matsalolin rashin adalci da tsarin siyasa ya haifar a cikin jam’iyyar su a wancan lokaci.
Sai dai ya bayyana cewa ba ya fitar da ran cewa shi da Kwankwaso za su sake hadewa a lema daya ta siyasa a nan gaba.
Sai dai Shekarau ya yi nuni da muhimmancin yin adalci a siyasa, wanda a cewar sa, shi ne ke kawo zaman lafiya da ci gaba a jam’iyya.