Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

0
84
Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta maka jaridar Daily Trust a kotu, tare da shigar da ƙorafi game da ita, a gaban ƙungiyar masu gidajen jarida ta Najeriya saboda abin da ta ƙira ”yaɗa kalaman neman tayar da rikici da karya aikin jarida”

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin tana sane da yadda a cikin ‘yan watannin baya, jaridar Daily Trust ke yaɗa labaran da ke neman gogawa gwamnatin kashin kaji.

Da ya ke magana a wajen wani taron manema labarai a ranar Asabar, ministan yaɗa labaran ya kafa hujja da labaran da jaridar Daily Trust ta wallafa a game juyin mulkin Nijar, da wanda ya ce jaridar ta rubuta a kan shirin sauya sunan titin Murtala Muhammad da ke Abuja zuwa Wole Soyinka da kuma na baya bayan nan a game da sanya hannu a kan yarjejeniyar da ta shafi amincewa da auren jinsi.

KU KUMA KARANTA: Alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya ta haramta a Iraƙi

Ya yi bayanin cewa a dukkan labaran, gwamnatin ta gano yadda jaridar ta bayar da rahoto ba tare da gabatar da hujja ko shaidun zargin da ta yi ba, lamarin da kuma gwamnatin ke kallo a matsayin wani yunƙuri na wallafa ƙarya domin tunzura jama’a.

Ya ce: ‘’Ba mu taɓa tunanin Daily Trust da mutanen da ke da ita za su kai wannan mataki ba wajen neman tayar da rikici a ƙasar nan, ta hanyar zargin cewa gwamnati ta sanya hannu a kan yarjejeniyar tallata auren jinsi. Wannan tsabar zalunci ne saboda babu wannan tanadi a cikin yarjejeniyar.’’

Ministan ya koka da yadda wannan labarin ya janyo huɗuba mai zafi daga wasu malaman addini da kuma jefa jama’a cikin halin ɗarɗar, wanda kuma ya ce jaridar ce ta janyo.

KU KUMA KARANTA: Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi

Saboda haka, ministan ya ce ‘’Gwamnatin tarayya za ta bi duk hanyoyin da doka ta amince da su, domin neman haƙƙi a kotu.’’

Leave a Reply